Dr. Zainab Bagudu ta samu kyautar shugabanci na shekarar 2019
Kamfanin Igebere TV ta ba Mai dakin gwamnan jihar Kebbi, Dr. Zainab Shinkafi Bagudu, ta tabbata a matsayin wanda za ta lashe kyautar shugabanci na wannan shekarar da aka shirya.
Za a yi bikin bada wannan kyauta ne a Ranar 29 ga Watan Nuwamba a dakin taro na Sheraton Hotel da ke babban birnin tarayya, Abuja. Jaridar Leadership ta rahoto haka a Ranar Laraba.
Jami’an Igbere TV sun ziyarci Mai girma Zainab Shinkafi Bagudu inda su ka tabbatar mata da wannan ta bakin Honarabul Mascot Uzor Kalu wanda ya jagoranci kwamitin gudanar da bikin.
Mascot Uzor Kalu ya bayyanawa Manema labarai cewa sun tantance Uwargida Zainab Shinkafi Bagudu a matsayin wanda za ta lashe kyauta a rukunin zaman lafiya na wannan shekara ta 2019.
Matar gwamna na Kebbi za ta karbi kyautar ne a Ranar 29 ga Nuwamba a matsayin Uwargidar gwamnan da ta fi kokari a kan fannin kiwon lafiya saboda irin kokarin da ta ke yi a jihar ta
KU KARANTA: Zaben Jihar Bayelsa ya jawowa Jonathan zargi a Jam'iyyar PDP
Igebere TV ta jinjinawa tsare-tsaren da Mai dakin shugaban gwamnonin na APC ta kawo a jihar Kebbi domin inganta harkar kiwon lafiya. Tun asali dama Zainab Bagudu kwararriyar Likita ce.
Daga cikin sauran wanda za a karrama tare da matar Gwamnan akwai gwamnonin jihohi, ‘yan kasuwa, masu rike da mukamai, Attajirai, kungiyoyi da kuma sauran masu yi wa kasa hidima.
Wadanda da ake tunani za su iya lashe wannan kyaututtuka a shekarar nan akwai: Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, Sanata Ahmed Lawan, Linda Ayade, Femi Adesina, da Nkeiruka Onyejiocha.
Saura sun hada da tsohon gwamna Ibrahim Dankwambo, da Ministoci Gordy Uche da Godswill Akpabio. Dr. Uche Ogah, SSA Ita Enang, tsohon 'dan wasa Kanu Nwankwo, da Mista Kalu Uche.
Za a samu rukunan kyaututtuka da su ka hada da ‘dan majalisar shekara, ‘dan gwagwarmayar shekara, gwamnan shekara, Sanatan shekara, daga cikin wadannan manyan mutane fiye da 20.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng