Tonan silili: Fasto ya tilasta amarya ta cire kayan amarci saboda an taba kwanciya da ita

Tonan silili: Fasto ya tilasta amarya ta cire kayan amarci saboda an taba kwanciya da ita

- Wata budurwa ta wallafa yadda wani fasto ya tozarta amarya a ranar bikinta

- Ya tambayeta ko an taba kwanciya da ita sai ta amsa mishi da cewa eh an taba

- A take ya umarceta da cire farar rigar daurin auren tare da bata mai launin ruwan madara ta sanya

Wata budurwa ta bada labarin yadda wani fasto ya tozarta wata amarya a ranar bikinta a wata coci dake garin Uyo cikin jihar Akwa Ibom.

Kamar yadda budurwar ta bada labari, lamarin ya faru ne a cocin inda ake shirin daurin auren amaryar da angonta. Faston ya tambayi amaryar ko budurwa ce, amma sai ta amsa mishi da a’a. A take kuwa faston ya bada umarnin ta cire farar rigar daurin auren tunda ba budurwa ba ce.

Faston ya musanya mata da riga mai launin ruwan madara wacce ya umarceta da ta sanya saboda ba budurwa ba ce, wannan abu da Faston yayi shine karshen tozarci a wajen wannan amarya.

KU KARANTA: Kwamacala: Saurayi dan shekara 31 ya auri kakarsa mai shekaru 91

“Wata yarinya da na sani ta yi aure a garin Uyo cikin jihar Akwa Ibom a ranar Asabar. A gaban jama’ar da ke cocin faston ya tambayeta ko ita budurwa ce amma sai ta amsa da a’a. A take kuwa ya umarceta da cire farar rigar da ta sanya don daurin auren inda ya bata mai launin ruwan madara don ta saka.

“A kan me fasto zai tozarta amarya kamar haka, a kuma ranar bikinta? Na tausaya mata kuma naji haushi. Haka ita kanta ta dinga dariyar yake wacce bata kai zuci ba a ranar.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng