Zaben gwamnan Kogi: Dalilai 4 da suka saka PDP ta sha kaye a hannun APC

Zaben gwamnan Kogi: Dalilai 4 da suka saka PDP ta sha kaye a hannun APC

A ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba ne Hukumar Zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da cewa dan takarar jam'iyyar APC a jihar Kogi, Yahaya Bello ne ya lashe zabe.

A cewar INEC, ya samu kuri'u 406,222 inda ya kayar da Musa Wada na jam'iyyar PDP dake biye da shi da kuri'u 189,704.

Legit.ng ta yi fashin baki kan dalilan da suka janyo wa PDP shan kaye a jihar.

1. Matsaloli yayin zaben cikin gida

Zaben cikin gida da aka gudanar a jam'iyyar PDP a jihar Kogi bai gamsar da mafi yawancin 'yan takara da masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam'iyyar ba.

Sanata Dino Melaye, daya daga cikin 'yan takara a jihar ya yi watsi da zaben cikin gidan kuma ya yi tir da sakamakon. Ya sha alwashin zuwa kotu don kallubalantar sakamakon amma daga bisani ya yi sulhu da wanda ya lashe zaben.

Abubakar Ibrahim Idris da ya zo na biyu a zaben shima ya nuna rashin amincewarsa ga zaben fidda gwanin.

2. Rasa tikitin takara da Dino Melaye ya yi

Wasu masu nazarin siyasa suna ganin Sanata Dino Melaye ya fi dan takarar gwamnan da PDP ta tsayar karbuwa a wurin mutane kuma akwai alamun zai iya kayar da Yahaya Bello idan da ya samu tikitin.

3. Rashin amincewar Dino Melaye ya jagoranci yakin neman zaben gwamna

A watan Satumba, Melaye ya bayyana cewa bai amince da tayin da aka masa ba a matsayin shugban yakin neman zabe na dan takarar gwamna na PDP a jihar duk da sulhun da ya yi da dan takarar.

Ko a lokacin zaben, Dino Melaye ya mayar da hankali ne wurin ganin ya yi nasara a zabensa bai wai na gwamnan ba duba da cewa a rana guda aka yi zabukan biyu.

DUBA WANNAN: An garkame wani dalibin jami'a a jihar Kano a kan caccakar dan majalisa

4. Mulki na hannun APC

Duk da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya hambarar da Jonathan daga mulki a 2015, abu ne mai wuya dan takara ya hambarar da wanda ke kan mulki a Najeriya duba da irin rawar da kudi ke takawa a siyasar Najeriya.

Babu shakka Gwamna Yahaya Bello dake kan mulki ya fi abokin takararsa kudi da kuma karfin iko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel