Jami’in kwastam da ya ki amsan cin hancin N 149,350,000 ya samu lambar yabo daga Buhari

Jami’in kwastam da ya ki amsan cin hancin N 149,350,000 ya samu lambar yabo daga Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama wani babban jami’in hukumar kwastam, Bashir Abubakar, mai mukamin mataimakin kwanturolan kwastam sakamakon kin karbar cin hancin makudan kudi da masu fasa kauri suka bashi.

Shi dai Abubakar ya ki amincewa da cin hancin $412,000, kimanin N149,350,000 da wasu mutane suka bashi kimanin shekara 1 da ta gabata domin su shigo da sundukai guda 40 na kwayar nan mai sa maye watau Tramadol.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun tarwatsa gungun mayakan Boko Haram, sun kwace makamai

Da wannan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Abubakar a matsayin jadakan yaki da rashawa, kuma wanda ya zamto abin koyi a tsakanin sauran jami’an hukumar da ma yan Najeriya gaba daya.

A shekarar data gabata ne wasu miyagun mutane suka shigo da sundukai guda arba’in da daya (41), dake makare da kiyagun kwayoyin Tramadol ta tashar jirgin ruwa na Apapa dake jahar Legas.

Sai dai bayan an kama kwayoyin sai yan kasuwan da suka shigo dasu suka nemi shugaban tashar jirgin ruwan, Kwanturola Bashir Abubakar tare da bashi cin hancin $420,000, kimanin N149,000,000 kenan da nufin ya sakar musu kayansu.

Amma Allah Yasa Bashir Abubakar mutum ne mai tsoron Allah, sai ya tsaya kai da fata yace ba zai karbi wadannan haramtattun kudade ba, kuma ba zai saki haramtattun kwayoyin ba sakamakon suna lalata rayuwar matasa, musamman matasan Arewa.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Buhari ya nemi majalisun dokokin Najeriya su yi gaggawar kammala aiki a kan kudurin dokar kafa kotunan da zasu hukunta manyan laifuka na musamman.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a yayin wani taro mai taken “Raguwar cin hanci da rashawa a aikin gwamnati” wanda hukumar yaki da rashawa ta ICPC da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta shirya a babban birnin tarayya Abuja.

A jawabinsa, Buhari ya roki bangaren shari’a su amince da wannan kuduri tare da bayar da goyon bayansu don ganin an samar da wadannan kotuna wanda yan Najeriya ke kira a kafasu domin su hukunta laifukan cin hanci da rashawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel