Yanzu Yanzu: Anyi jana’izar mutum 18 da yan bindiga suka kashe a Katsina

Yanzu Yanzu: Anyi jana’izar mutum 18 da yan bindiga suka kashe a Katsina

Anyi jana’izar mutum 18 da yan bindiga suka kashe a kauyen Yar Gamji da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina a safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu a makabartan Dan Takum bayan anyi sallar gawa a fadar sarkin Katsina.

Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, tare da hakimai da masu rike da sarauta da dama, da kuma jami’an gwamnati na daga cikin daruruwan mutanen da suka halarci jana’izar.

Babban limamin masallacin Juma’a na Katsina, Ustaz Mustapha Ahmed, ne ya jagoranci sallar gawan, yayi addu’a kan Allah ya ji kansu sannan ya ba iyalansu da abokansu juriyar wannan rashi.

Da yake jawabi jim kadan bayan jana’izar, hakimin Batsari, Mannir Rumah, ya bayyana bukatar jami’an tsaro su kare rayuka da dukiyoyin jama’a yadda ya kamata.

Yanzu Yanzu: Anyi jana’izar mutum 18 da yan bindiga suka kashe a Katsina
Yanzu Yanzu: Anyi jana’izar mutum 18 da yan bindiga suka kashe a Katsina
Asali: UGC

Yayi kira ga mazauna yankin da su kasance masu sanya idanu sannan sub a hukumomin doka hadin kai ta hanyar taimaka masu da bayanai masu amfani akan ta’addanci.

A nashi jawabin, Shugaban karamar hukumar Batsari, Manir Ma’azu, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki, cewa “babu banbanci da abunda muka saba yi.

“Yan bindiga na kai mana hari duk dare amma wannan ya faru ne da safe lokacin da suka kai hari gonakin,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Wata motar BRT ta kama da wuta a gadar third mainland

“Akwai iyaka a abunda za mu iya yi; muna tuntubar yan sanda amma da wuya ka gansu suna daukar mataki a lokacin da ake bukatarsu sosai,” cewar sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng