Abdullahi Danbaba: Majalisar dattawa ta rantsar da sabon Sanata

Abdullahi Danbaba: Majalisar dattawa ta rantsar da sabon Sanata

- Majalisar dattawa ta rantsar da Abdullahi Danbaba, sanata mai wakiltan Sokoto ta kudu

- Danbaba wanda ya fito daga jam’iyyar PDP, ya maye gurbin sanatan APC, Shehu Tambuwal wanda kotun daukaka kara ta sallama

- Daga cikin tsarin rantsarwar, Danbaba ya dauki rantsuwar kama aiki a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba a zauren majalisa

Majalisar dattawa a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, ta rantsar da Sanata Abdullahi Danbaba mai wakiltan Sokoto ta Kudu.

Danbaba na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya maye gurbin Shehu Tambuwal (daga All Progressives Congress) wanda kotu ta sallama a kwanan nan.

Dan majalisar na PDP ya kuma dauki rantsuwar kama aiki a lokacin bikin rantsarwar.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kogi: Dino Melaye ya yi barazanar kai karar Gwamna Yahaya Bello gaban ICC

Ku tuna jam’iyyar Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, kotun daukaka kara ta tsige Tambuwal, mai wakiltan Sokoto ta kudu a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Alhamis, 14 ga Watan Nuwamban 2019, Sanata Abiodun Olujimi ta koma kujerarta a majalisar dattawa. Kamar yadda mu ka samu labari Sanatar ta yi rantsuwar shiga ofis.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, shi ne ya rantsar da Biodun Olujimi inda za ta cigaba da wakiltar Mazabar jihar Ekiti ta yamma a majalisa ta tara.

Biodun Olujinmi ta maye gurbin Sanata Adedayo Adeyeye wanda kotu ta karbe kujerarsa. Kotun daukaka kara da ke zama a Garin Kaduna ta ba 'Yar takarar adawar gaskiya a shari’ar zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng