Lawan: Inda wannan Majalisar ta sha ban-ban da wadanda su ka shude a baya

Lawan: Inda wannan Majalisar ta sha ban-ban da wadanda su ka shude a baya

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya yi bayani a game da abin da ya sa Sanatocin kasar su ka hadu su ke aiki da juna duk da banbancin jam’iyya da ra’ayin siyasar su.

Ahmed Lawan ya yi wannan jawabi ne a wajen wata liyafa da jami’ar tarayya ta Maiduguri ta shirya a karshen mako. Lawan ya na cikin fitattun wadanda su ka yi karatu a wannan jami’a.

Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya ke cewa majalisar da ya ke jagoranta a yau ta na da banbanci da sauran duk majalisun da aka yi a da, domin kuwa ba a la’akari da sabanin siyasa a wajen aiki.

“Mun zabi mu hada-kai a abu guda; wannan shi ne kishin kasa. Babu banbancin jam’iyyar siyasa. Za ka iya zama ‘Dan jam'iyyar APC a majalisa, z aka iya zama ‘Dan PDP a majalisar tarayya.”

Ahmed Lawan ya cigaba da cewa: “Kai! Za ka iya zama ‘Dan jam’iyyar YPP a majalisar tarayya. A wannan majalisa mai-ci, musamman ta Dattawa, jam’iyyunmu ne su ka kai mu inda mu ka kai.”

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun hadu da Goodluck Jonathan har gida

“Mu na godewa jam’iyyunmu, kuma mun yarda da akidu da muradun jam’iyyun, amma mun hadu a kan cewa za mu dunkule mu yi wa Najeriya aiki.” Inji Shugaban majalisar dattawan kasar.

Shugaban majalisar ya ce jama’a da-dama ba su fahimci aikin majalisa ba saboda ita ce ‘yar autar bangarorin gwamnati, tare da karawa da cewa burinsu shi ne a samar da tsaro da inganta tattali.

Lawal ya ce: Ubangiji ya yi wa dukkaninmu gyadar doguwa. Wasu sun fi wasu samun alfarma a cikinmu, amma dai wadanda ba su samu wannan rabo ba, su ne wadanda su ke waje a Kauyuka.

‘Dole mu yi masu kokari na ganin mun canza masu rayuwa. Aikin mu ne kuma nauyin mu ne yin abin da ya kamata ba tare da nuna banbancin siyasa ba. Za mu yi fada, kuma mu shirya a nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel