Na fi asalin ‘yan daudu kwarewa wajen iya daudu a fim – Ado Gwanja
- Fitaccen jarumi kuma mawakin Hausa Ado Gwanja ya bayyana cewa tsabar iya kwaikwayon yan daudu a cikin fim ne ya sa ake bashi wannan matakin yake hawa a wasanni
- Gwanja ya ce duk wani mutum da ya san shi sosai ya san bai da nasaba ko kadan da yan daudu
- Ya bayyana cewa wani fim ne ya kama ana bukatar yan daudu amma sai duk suka kasa, don haka da aka gwada shi asai aka ga ya fi su kwarewa
Shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma fitaccen mawaki, Ado Gwanja ya bayyana cewa tsabar iya kwaikwayon yan daudu a cikin fim ne ya sa ake bashi wannan matakin yake hawa a wasanni.
A wata hira da shafin BBC Hausa ta yi da jarumin, Gwanja ya ce duk wani mutum da ya san shi sosai ya san bai da nasaba ko kadan da yan daudu a gaske.
A cewarsa: “aiki ne za mu yi na fim da ya shafi daudun aka kira 'yan daudun sun fi su 50 amma suka kasa yi.
"To sai aka ce bari a gwada dan masana'antar Kannywood din, da aka gwada sai aka ga na ma fi su iya kwaikwayon abin sosai, shi kenan tun daga lokacin sai kuma ake yawan sa ni."
Gwanja ya fara ne daw aka, sai dai daga farko da ya ga ba ta karbu ba sai ya hada da fitowa a fina-finai.
Yawanci wakokin Gwanja sun fi farin jini a wajen mata saboda yadda yake wasa su, ya kuma ce yana hakan ne saboda "mata aka fi sani da son biki, to idan ba ka wasa su ba wa za ka wasa?"
KU KARANTA KUMA: Zaben Bayelsa: Buhari ya taya zababben gwamnan Bayelsa David Lyon murna
Gwanja ya karyata zagin cewa yana sa kalmomin batsa a wakokinsa, yana mai cewa da Hausa yake wakar ba wani yare ba, "kuma a sanina Bahaushe na da fahimta, kuma idan aka dauko wakokina a ka zube ba wacce ta shafi batsa."
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng