Kotun daukaka kara ta jaddada tsige sanatan APC da dan majalisar wakilai

Kotun daukaka kara ta jaddada tsige sanatan APC da dan majalisar wakilai

Kotun daukaka kara, da ke zama a Sokoto ta tabbatar da Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa da Dr. Balarabe Shehu Kakale na jam’iyyar Peoples Democratic Party a matsayin wadanda suka lashe zaben majalisar dokokin tarayya a yankin Sokoto ta kudu da mazabar Bodinga/Dange-Shuni/Tureta.

Sanata Abubakar Shehu Tambuwal da Aliyu Shehu AA wadanda kotun daukaka kara ta tsige a ranar 30 ga watan Oktoba be suka shigar da karar wanda kotu ta yi watsi dashi a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba.

Da yake zartar da hukunci alkalin kotun, Justis Ibrahim Musa Saulawa, ya ce kotun bata da hurumin sauraron karar.

“Da zaran an saurari kara da aka daikaka sannan wannan kotun ta yanke hukunci toh ba za ta sake bi ta kan sa ba,” in ji shi.

Don haka Justis Saulawa, ya kori karar sannan ya ci tarar wadanda ke karan N50,000.

A wani lamari makamancin haka, kotun daukaka karar, ta kori karar da ke kalubalantar zaben shugaban majalisar dokokin jihar Sokoto, Bello Musa Ambarura da wasu yan majalisa hudu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar kan rashin inganci.

Sauran yan majalisar sune Hon. Muhammadu Bello Idris mai wakiltan mazabar Gwababawa ta arewa; Hon. Abdullahi Garba Sidi mai wakiltan Gwadabawa ta kudu da kuma Hon. Aminu Magaji Bodai, mai wakiltan mazabar Dange-Shuni sai kuma Hon. Faruku Ahmad mai wakiltan mazabar Goronyo.

Yan takarar PDP ne suka shigar da dukkanin kararrakin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon ministan labaran Najeriya rasuwa

Sai dai kuma yan takarar PDP uku ma sun yi nasara kotun bayan ta yi watsi da kararrakin da APC da yan takararta suka daukaka.

Yan majalisar sune, Hon. Mohammed Malami Ahmed mai wakiltan mazabar Sokoto ta Kudu 1, Hon. Halliru Buhari mai wakiltan Sokoto ta arewa 1 da kuma Hon. Romo Sule Hantsi mai wakiltan mazabar Tambuwal ta yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel