An kori ma'aikatan lafiya 10 a kan laifin siyar da jinin da jama'a ke bada wa tallafi

An kori ma'aikatan lafiya 10 a kan laifin siyar da jinin da jama'a ke bada wa tallafi

Ma'aikatan lafiya 10 na asibitin Dalhatu Araf, da ke Lafia a jihar Nasarawa aka kora akan satar jinin da jama'a ke bada wa tallafi don marasa lafiya. Suna siyar da jinin ne inda suke soke kudaden. Bayan haka, an kamasu da laifin almundahanar wasu kudade.

Dr Hassan Ikrama, shugaban asibitin, ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a ranar Alhamis a garin Lafia.

"Wasu daga cikinsu an kamasu da laifin satar jinin da mutane suka bada don tallafawa marasa lafiya tare da siyarda shi ga asibitocin kudi, da kuma waskar da wasu kudaden asibitin."

Wasu na amfani da kayayyakin aikin asibitin don bincike a sashin binciken asibitin, amma sai su kalmashe kudin zuwa aljihunsu.

Ya tabbatar da cewa, duk ma'aikatan da a ka kora, sai da wani kwamiti ya bincikesu kuma ya tabbatar da laifukansu sannan korar ta biyo baya.

Ikrama yace, lokacin da aka nada shi matsayin shugaban asibitin, ya gano baraka masu tarin yawa ta bangaren kudin asibitin, abinda ya kamata a duba.

DUBA WANNAN: An tura dan majalisa gidan yari saboda dukan wata mata

"A maimakon a samu karuwa ta wajen kudin shigar asibitin, ma'aikatan na ta kokarin waskar da su don amfaninsu, a dalilin haka ne kuwa abubuwa da dama na asibitin ke yin kasa a kullum. A lokacin da nazo, asibitin na fama da rashin na'urori da yawa, dakin tiyata daya garesu, gadaje 200 kacal suke da su, dakin shan magani daya kuma babu isassun ofishin likitoci."

"A don haka ne, da yawan marasa lafiyan muke tura su Jos, asibitin tarayya na Keffi ko asibitin kasa na Abuja, saboda rashin isassun kayan aiki," in ji shugaban asibitin.

Ikarama yace, hukumar asibitin cikin kankanin lokaci ta kawo cigaba, inda ta kara dakunan tiyata biyu, dakunan shan magani 8, na'urar hoto 8. Ta kara gadaje 200, gyaran dakunan kwantar da mutane, bandakuna da sauransu.

Ya kara da cewa, an kara daukar wasu kwararrun ma'aikata aiki don karfafa aiyukan.

A halin yanzu muna da manyan likitoci 40 kwararru a bangare daban-daban, sama da likitoci 100 banda malaman jinya, masu hada magani da sauransu.

Ikrama ya kara tabbatar wa da muatne cewa, asibitin zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin sun gamsar da mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng