Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan' (Hotuna)

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan' (Hotuna)

Wani addini mai suna 'Yarsan' na daya daga cikin tsoffi kuma daddun addinai a yankin Gabas ta tsakiya. Ana kiran addinin Ahl-e Haqq da harshen Larabci, ma'anarsa kuwa itace "Ma'abota gaskiya".

A kiyasi dai, addinin Yarsan na da mabiya a kalla miliyan uku a kasar Iran, wadanda da yawansu mazauna yammacin kasar inda Kurdawa ke da rinjaye ne. A kasar Iraqi kuwa, an fi kiransu da suna Kaka'i kuma akwai mabiya addinin da zasu kai 120,000 zuwa 150,000, kamar yanda BBC Hausa ta ruwaito.

Wurin bautar ma’abota addinin na yankin Kermanshah ne da ke yankin Iran. Addinin ya samo asali ne tun karni na 14 ko 15 kuma yana kama da mazhabar Shi’a. Addinin na da littafi mai suna Kalam-e Saranjam, wanda aka dora kan koyarwar Sultan Sahak.

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan'
Wajen bautar ma'abota addinin Yarsan
Asali: Facebook

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan'
Mabiya addinin Yarsan yayin bikin addini
Asali: Facebook

Mabiya addinin Yarsan na amfani da goge a lokutan bukukuwan addini da suke kira da “tanbur” tare da rera wasu baituka da kalamai da ake kira da “kalam”.

DUBA WANNAN: Yadda dalibin jami'ar Legas ya harbi wani mutum a mazakuta

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan'
Mabiya addinin Yarsan a taron "Jam"
Asali: Facebook

Ma’abota addinin Yarsan na yin taro duk wata a wani wuri da suke kira da “jamkhaneh”. Ana kiran taron da “jam”. Duk wanda ya shiga taron jam kuwa, dole ne ya bi wasu ka’idoji, ciki kuwa har da sa wata hula ta musamman. Suna yin da’ira tare da kallon wani guri da aka kebe don hakan a cikin jamkhaneh, kamar yanda BBC Hausa ta ruwaito.

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan'
Yarsani na yin azumi uku a watan Aban
Asali: Facebook

Yarsani na yin azumi uku a watan aban a cikin jerin watannin da kasar Iran ke amfani dasu, wanda yake fara wa daga watan Oktoba zuwa Nuwamba.

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan'
Addu'ar jam'in Yarsani bayan shan ruwa
Asali: Facebook

A duk lokacin da mabiya addinin Yarsan suka yi azumi, suna gabatar da addu’ar jam’I a daren yayin da suke shan ruwa idan rana ta fadi.

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan'
Gashin baki a matsayin alamar daukaka ga mabiya addinin Yarsan
Asali: Facebook

A duk lokacin da mabiya addinin Yarsan suka yi azumi, suna gabatar da addu’ar jam’i a daren yayin da suke shan ruwa idan rana ta fadi.

Labarin wani addini da ba a san shi ba mai suna 'Yarsan'
Kundin tsarin mulkin Iran bai aminta da addinin Yarsan ba
Asali: Facebook

Amma kuma, kundin tsarin mulkin Iran bai aminta da mabiya addinin Yarsan ba. A maimakon haka, ana kallonsu a matsayin mabiya mazahabar Shi’a da ke bin tafarkin sufaye. Duk da haka, wasu daga cikin malaman Shi’a na kallonsu a matsayin wadanda basu yi Imani da mazhabarsu ba.

Mabiya addinin basu yin zaman makoki in anyi musu rasuwa, hakan kuwa yasa suka gagara yi wa ‘ya’yansu takardar shaidar haihuwa . Suna sanarwar cewa, ba a bas u damar wallafa littafan addinisu ba. Sannan ana hukuntasu idan suka ci zarafin addinin musulunci ko kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164