Sheikh Dahiru Bauchi ya ce masoya Annabi ne ke yin Maulidi

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce masoya Annabi ne ke yin Maulidi

- Wani bangare na al'umman Musulmi na tsaka da bikin Maulidin Annabi Muhammadu Sallahu alaihi wasallam

- Babban malamin darika, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce mosaya Annabi ne ke raya wannan lokaci na haihuwar fiyayyen halitta

- Dahiru Bauchi ya ce shauki da soyayyar Manzon Allah ne ya kawo haka

Kamar yadda muka sani wasu rukunin Musulmi a duniya irin mabiya darika da qadiriya na gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallam.

An dai haifi Annabi Muhammad a ranar 12 ga watan Rabiul-Awwal, wanda shi ne wata na uku daga cikin jerin watannin Musulunci guda 12.

Don haka yayinda aka zanta da babban malamin addinin Islama kuma Shugaban mabiya darika, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa, watan Rabi’u Awwal ya samu daraja ne saboda a cikinsa ne aka haifi Manzan Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Dahiru Bauchi ya kara da cewa, “masoya Annabi da ke damuwa da shi, su suke yin a Maulidi”.

Ya ce kowani Musulmi na murna da wannan wata saboda a cikinta ne aka haifi mafi daraja wanda ya kawo mana abu mafi daraja da girma. Ya ce darajar abunda ya kawo Maulidi shine haifar Annabi da aka yi a cikinta.

Malamin ya ce maulidi na da ma’ana biyu a larabce wato wurin da aka haifi mutum da kuma water da aka haife shi. Hakan ne ya sa aka ce ayi Hajj da Umrah wato Maulidin garin da aka haifi fiyayyen hallita kenan, sannan Maulidi na wata kuma shine wanda ake yi yanzu.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Gwamna Ganduje ya caccaki sarki Sanusi

Ya ce ana yin Maulidi ne domin gode wa Allah akan ni’mar da ya yi mana na bamu fiyayyen halitta. Ya ce duk masu sukar Maulidi basu da wata hujja na yin haka.

Ya kara da cewa bege da shauki ne ya sanya masoyan Annabi yin Maulidi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel