Jami’an tsaro sun samu Fitaccen Masanin tarihi Sokolov da jikin wata Baiwar Allah

Jami’an tsaro sun samu Fitaccen Masanin tarihi Sokolov da jikin wata Baiwar Allah

Fitaccen Masanin tarihin nan na kasar Rasha, Oleg Sokolov, ya ga ta kansa bayan da aka yi ram da shi dauke da kafadu biyu na wata mata. An samu sashen matar ne a cikin jakar goyonsa.

Kamar yadda rahotanni su ka same mu daga Jaridar Moscow Times, wani Shehin Malami watau Oleg Sokolov, ya amsa da bakinsa cewa shi ya kashe wannan mata da ta yi karatu a hannunsa.

Farfesa Oleg Sokolov mai shekaru 63 a Duniya ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda ne a gabar rafin Garin St. Petersburg da ke kasar Rasha inda aka same shi dauke da kafadun wannan Mata.

‘Yan sanda sun garkame Farfesan tun jiya Ranar 9 ga Watan Nuwamban 2019, bisa zargin kisan kai. Jami’an tsaron sun ce sun biyo shi ne tun daga rafin Moika tare da kafadun da ya kacalcala.

A cewar ‘yan sandan, sun laluba gidan Sokolov, inda su ka samu gawar tsohuwar ‘dalibarsa a jami’a, Anastasia Yeshchenko mai shekaru 24, wanda su ka yi aiki tare da shi a lokuta da-dama.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun mika wuya gaban Sojojin Najeriya

Lauyan wannan Malami, Alexander Pochuyev, ya fadawa Interfax cewa wanda ake karar ya amsa laifinsa da cewa shi ya yi wannan kisa. Lauyan ya ce wasu abubuwa ne su ka tunzura Shehin.

“Sokolov ya yi abin da ya yi ne a karkashin tasirin wani abu. A yanzu sai dai kurum mu yi ta hasashe.” Lauyan Malamin ya fadawa ‘yan jaridar kasar Rasha a lokacin da ya zanta da su jiya.

‘Yan jaridan St. Petersburg sun rahoto cewa ana zargin Sokolov ya yi yunkurin jefa gawar tsohuwar ‘Dalibar ta sa ne a rafi. Sokolov ya yi fice wajen bincike a kan Napoleon Bonaparte.

A shekarun baya wata ‘Dalibar wannan Malami ta taba fitowa ta zarge shi da kokarin kashe ta. Jama’a da dama dai sun fito su na Allah-wadai da Malamin yayin da ake shirin shiga kotu da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel