Rufe iyakokin Najeriya: Buhari ya yanke shawara mai kyau – Jigon PDP

Rufe iyakokin Najeriya: Buhari ya yanke shawara mai kyau – Jigon PDP

- Wani jigon jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), Cif Sunny Onuesoke ya bayyana rufe iyakokin Najeriya a matsayin shawara mafi kyau da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a yan baya-bayan nan

- Onuesoke ya jaddada cewa hukuncin Buhari na rufe dukkanin iyakokin kasar shine shawara mafi kyau domin cigaban tattalin arzikin kasar

- Ya kara da cewa duk wahalar da za a shiga a yanzu na dan lokaci ne, domin mutane za su dara a gaba

An bayyana rufe iyakokin Najeriya a matsayin shawara mafi kyau da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a yan baya-bayan nan.

Jigon jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Cif Sunny Onuesoke, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 8 ga watan Nuwamba, ya jaddada cewa hukuncin Shugaban kasa Buhari na rufe dukkanin iyakokin kasar shine shawara mafi kyau domin cigaban tattalin arzikin kasar.

Ana tsaka da samun korafe-korafe daga yan Najeriya kan tsadar kayayyakin abinci irin su shinkafa a kasuwanni, jigon na PDP ya yi hasashen cewa wahalar da ake ciki a yanzu zai zama tarihi nan gaba domin za a dara.

Onuesoke, yayinda yake zantawa da manema labarai a Warri, jihar Delta, ya bayyana cewa rufe iyakar kasar zai tursasa gwamnatin Najeriya ta magance wasu lamura masu muhimmanci a tattalin arzikin kasar.

Ya kara da cewa rufe iyakokin ya kasance wani dama domin karfafa wa masu samar da kayayyakin gida gwiwar kara kaimi wajen aikinsu da kuma samar da ingantattun abubuwa daga cikin lamarin.

“Idan muka rufe kofofin shigo da kayayyaki daga waje, za a koma siyan na gida sosai.

“Ta haka, ana habbaka kayayyakin cikin gida, samar da ayyuka ga mutanenmu sannan kuma a lokaci guda ana koran talauci,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kogi: Manyan yan takara 5 da ka iya samun shiga gidan gwamnati

Onuesoke ya jaddada cewa rufe iyakar ya nuna karfin yan Najeriya wajen samar da wasu daga cikin kayayyakin amfaninsu kamar shinkafa da kifi, inda ya kara da cewa idan har yan kasar suka cigaba da haka, shakka babu kasar za ta zama mai dogaro da kai a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel