An bankado cikakken sunayen hadimai 35 da Buhari ya fatattaka daga ofishin Osinbajo

An bankado cikakken sunayen hadimai 35 da Buhari ya fatattaka daga ofishin Osinbajo

Jaridar Daily Trust ta samo cikakken jerin sunayen hadiman mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallama daga aiki, tare da mukamansu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin jerin sunayen hadiman Osinbajo akwai Ajibola Ajayi, diyar tsohon gwamnan jahar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi wanda it ace hadimar Osinbajo ta musamman a kan harkar shari’a.

KU KARANTA: Maulidi: Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Litinin a matsayin ranar hutu

Akwai Lanre Osinbona, babban mataimaki na musamman a kan sadarwar zamani, Imeh Okon babban mataimaki na musamman a kan manyan ayyuka, Jide Awolowo babban mataimaki na musamman a kan harkar mai da iskar gas, Gambo Manzo mataimaki na musamman a kan harkar siyasa, Edobor Iyamu babban mataimaki na musamman a kan Neja Delta.

An bankado cikakken sunayen hadimai 35 da Buhari ya fatattaka daga ofishin Osinbajo
An bankado cikakken sunayen hadimai 35 da Buhari ya fatattaka daga ofishin Osinbajo
Asali: Twitter

A yanzu dai rahotanni sun fara yawo cewa wannan wata makarkashiya ce ake shirya ma Osinbajo don ganin bai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 ba.

Haka zalika rahotanni sun tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasa na da hadimai 80, don haka wasu shafaffu da mai suka kitsa ma shugaban kasa cewa lallai ya rage masa karfi ta hanyar daukan wannan mataki.

Masana da dama suna kwatanta wannan bahallatsa kamar abin da ya faru a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Obasanjo da mataimakinsa Atiku Abubakar, musamman lokacin da ruwa ya yi tsami a tsakaninsu.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da sallamar hadiman, inda tace daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya aka aika musu da takardun sallama daga aiki, amma kuma wasu majiyoyin daga Villa sun ce Osinbajo ya amshe takardun gaba daya daga hannayensu, yana jiran dawowar shugaba Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel