Bincike: Ministan kasuwanci ya hada kai da CAC an yafewa Banki wasu kudi

Bincike: Ministan kasuwanci ya hada kai da CAC an yafewa Banki wasu kudi

Ana zargin Mukaddashiyar shugabar hukumar CAC mai rajistar kamfanoni, Azuka Azinge, da hada kai da tsohon Ministan harkar kasuwanci da masana’antun Najeriya, wajen yin ba daidai ba.

Kamar yadda mu ke samun rade-radi daga Daily Nigerian, Azuka Azinge da Okechukwu Enelama sun jawowa Najeriya asarar Naira miliyan 559. Wannan badakala ta faru ne a cikin shekarar 2018.

Binciken da jaridar Daily Nigerian ta yi, ya bayyana cewa Messrs Azinge da Enelamah sun ba wasu kamfanoni lamunin da bai dace ba. Wadannan kamfanoni sun hada da wani babban banki.

Gwamnatin tarayya ta kan yi wa wasu kayyadadun kamfanoni afuwa wajen rajista idan hara bin da su ke yi zai taimakawa tattalin Najeriya. Sai dai wannan ya faru ne ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar ta CAC ta yafewa wannan bankin kudin da ke kansu ne a lokacin da su ka shirya buda hannun jarinsu daga Naira miliyan daya zuwa biliyan 25. A ka’ida ya kamata bankin su biya kudi.

Sai dai Ministan kasuwanci na lokacin da kuma shugabar CAR ta rikon kwarya sun shiga sun fita inda aka ki karbar kudin da su ka dace daga hannun bankin. Wannan kudi sun haura miliyan 180.

KU KARANTA: Dangote zai madai hankali wajen noman shinkafa a Najeriya

Wasu sakonni da su ka shiga hannun jaridar sun nuna yadda Ministan a lokacin da kuma Azinge su ka shirya yadda za su raba kazamin kudin da za a samu daga wannan badakala da aka tafka.

Sakon da shugabar ta CAC ta aikawa Ministan a Ranar 23 ga Watan Satumban 2018 ya na cewa:

“Further to our discussion yesterday on granting waiver for increase in share capital to Bank, may I suggest that you kindly send your approval by email to enable staff handling the transaction sight the authorization for the waiver."

“This will ensure smooth handling of the increase without audit query and delay. I will ensure speedy delivery accordingly.”

Washegari Okey Enelamah ya maida martani ya na mai amincewa da abin da aka shirya inda ya ce:

In the email response, the minister said: “Please accept this as my approval of the waiver as requested. Thank you.

Best regards, Okey Enelamah.”

Dayan kamfanin da ake zargi da aka yi wa irin wannan afuwa shi ne Enyimba Economic City Development Company Limited wanda aka janyewa nauyin biyan gwamnati miliyan 377.24.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel