PDP ta sha kaye a karar da ta daukaka kan Sanata Gobir, da yan majalisar wakilai 3 na APC a Sokoto

PDP ta sha kaye a karar da ta daukaka kan Sanata Gobir, da yan majalisar wakilai 3 na APC a Sokoto

Kotun daukaka kara a jihar Sokoto ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Salihu Maidaji ya daukaka akan zaben Sanata Ibrahim Gobir (APC, Sokoto ta gabas).

Maidaji ya daukaka kara akan hukuncin kotun zabe da ta kori kararsa sannan ta tabbatar da zaben Gobir. Kotun zaben ta riki cewa an shigar da karar a kurarren lokaci, sannan ta kore shi kan rashin hurumin sauraronsa.

Da yake zartar da hukunci, Justis Hamman Akawu Barka, yace kotun zaben ta yi daidai da ta yi watsi da karar kan rashin hurumin sauraronsa.

Don haka ya kori karar akan rashin inganci.

A halin da ake ciki, a hukunci na daban wanda ya kunshi mazabu hudu na tarayya, kotun daukaka karar ta tabbatar da zaben mambobin majalisar wakilai na APC uku da na PDP daya.

Yan majalisan na APC sune Abdullahi Salame mai wakiltan mazabar Gwadabawa/Illela; Architect Aliyu Almustapha (Rabah/Wurno) da kuma Abubakar Umar Yabo/Shagari.

KU KARANTA KUMA: Ku kasance masu gaskiya da wayewa - Ganduje ga sabbin kwamishinoni

Kotun daukaka karar ta kuma jaddada zaben dan PDP Mani Maishinko Katami mai wakiltan mazabar Binji/Silame.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel