Rashin aikin yi: Laifin ‘Yan Siyasa ne ba kowa ba – Inji Sarkin Legas

Rashin aikin yi: Laifin ‘Yan Siyasa ne ba kowa ba – Inji Sarkin Legas

Mai martaba Sarkin kasar Legas, Rilwan Akiolu, ya ce ‘yan siyasa ne silar rashin abin yi a Najeriya. Sarkin ya yi wannan jawabi ne a Ranar Asabar wajen yaye ‘daliban makaranta a Edo.

Idan ba ku manta ba a cikin karshen makon jiya ne aka yaye ’daliban jami’ar jihar Edo da ke Iyamho a cikin Garin Etsako. Mai martaba, Oba ne Legas ya na cikin wadanda aka gayyata taron.

Sarkin ya bayyana halin rashin aikin yin da ake ciki a Najeriya a matsayin ‘abin damuwa’, inda ya ce ‘yan siyasa sun soke Matasa a cikin aljihunansu ne ta hanyar ba su kudi maimakon abin yi.

Mai martaba Akiolu ya ke cewa ba a ba Matasa dukiyar da za ta yi masu amfani wajen habaka tattalin arzikin kasa. Sarkin ya ce: “A yadda mu ke tafiya da rashin aikin yi, abin akwai damuwa.”

KU KARANTA: Rufe iyakoki ba zai sa shinkafa ta gagara ba – Inji Manoma

“Duk da girmamawar da na ke yi maku, ‘yan siyasa, ku ne ku ke jawo wannan. ‘Yan kudin da ku (‘yan siyasa) ke ba Matasa su yi ihun babu wani sai ku, na wani ‘dan kankanin lokaci ne kawai.”

“Ku sani cewa ceto ya na hannun Ubangiji ne kurum ba kowa ba. Lokacin da zan shigo taron nan, na hangi Matasa su na ihun “Obaseki, Oshiomhole” kuma ba a Edo kadai ake irin wannan ba.”

Babban Sarkin kasar ya bayyana cewa kusan duk wata jihar Najeriya ana fama da irin wannan matsalar ta Matasa. Akiolu ya yi kira ga ‘yan siyasar su samar da wuta a ko ina a fadin Najeriya.

A jawabin na sa, Mai martaba Rilwan Akiolu ya yabawa kokarin gwamnatin jihar Edo. Sai dai kuma bayan taron wasu Matasa sun kai masu hari a rikicin siyasar da ake fama da ita a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng