Kasashen nahiyar Afrika biyar da suka fi samun cigaba

Kasashen nahiyar Afrika biyar da suka fi samun cigaba

Majalisar dinkin duniya ta ware wasu abubuwa da take amfani da su a matsayin mizani na auna cigaban kasa ko akasin haka. Dukkan wadannan abubuwa sun dogara da tattalin arzikin kasa, wanda shine ke kawo cigaban mutane da kuma kasa baki daya.

Kasashe biyar da aka bayyana sun samu cigaba a nahiyar Afrika idan aka kwatanta su da sauran takwarorinsu sun hada da;

1. Seychelles

Ana yin wa Sachille ganin kasar da tafi dukkan sauran kasashen Afrika arziki. Seychille wani yanki ne mai dauke da kasashe 115 a gefen gabashin Afrika ta gabas. Kasar ta cimma dukkan mizanin da ake amfani da su wajen auna cigaban kasa a karnin miladiyya.

Tattalin arzikin kasar Seychelle ya dogara ne da harkar noma, yawon bude ido da su (watau sana'ar kamun kifi).

Duk da kasancewar ta kasa ta farko ta fuskar cigaba a nahiyar Afrika, Seychelles ce kasa ta 63 a cikin jerin kasashen duniya 188 da suka cigaba.

2. Mauritius

Tattalin kasar Mauritius ya dogara ne a kan harkar noma, yawon bude ido da wasu aiyuka na musamman. Tana daga cikin kasashen Afrika da suka samu maki mai gwabi ta fuskar cigaban jama'a, hakan ba zai rasa nasaba da yawan masu saka hannu jari da suka bude masana'antu a kasar ba.

Kiyasi ya nuna cewa gama garin ma'aikaci a kasar Mauritania na samu a kalla dalar Amurka US$17,948 a kowacce shekara.

3. Tunisia

Tattalin arzikin kasar Tunisia ya dogara ne a kan masana'antu, aiyuka na musamman da kuma ma'adanai. Hukumar tattalin arziki ta duniya ta bayyana tattalin arzikin kasar Tunisa a matsayin mafi habaka a shekarar 2009.

DUBA WANNAN: Khadimul Islam: Ganduje ya kaddamar da shirin taimakon makarantun allo da islamiyya a Kano

Kasar Tunisia ta kasance kasa ta 97 a cikin jerin kasashen duniya 108 da aka bayyana sun samu cigaba a shekarar 2015.

4. Algeria

Algeria ita ce kasa mafi girma a nahiyar Afrika, kuma tattalin arzikinta, kamar na Najeriya, ya dogara ne a kan man fetur.

Ita ce kasa ta 83 a cikin jerin kasashen duniya da aka bayyana sun samu cigaba a shekarar 2019.

5. Afrika ta Kudu

Tattalin kasar Afrika ta Kudu shine na biyu a girma a nahiyar Afrika, Najeriya ce kadai keda girman tattalin arziki da ya wuce na kasar Afrika ta Kudu.

Noma da ilimin manyan makarantu na daga cikin manyan bangarorin da ke rike da tattalin arzikin kasar Afrika ta Kudu, kuma ita ce a mataki na 119 a jerin kasashen duniya da suka samu cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng