Labari mai dadi: Kwanan nan shinkafa za ta yi arha ta yadda ba za ta fi karfin talaka ba – Gwamna Bagudu

Labari mai dadi: Kwanan nan shinkafa za ta yi arha ta yadda ba za ta fi karfin talaka ba – Gwamna Bagudu

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ce albarkar da aka samu a fannin noma shinkafa a wannan daminar zai taimaka wajen daidaita farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya.

Bagudu, wanda ya kasance Shugaban kungiyar haraji na Shugaban kasa kan shinkafa da alkama a kasar, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwamba a karamar hukumar Argungu da ke jihar a yayinda yake zantawa da manoman shikafa a yankin.

“Albarkar da manoman shinkafa suka samu a wannan daminar zai karya farashin shinkafa yar gida domin hana fasa kaurin shinkafa yar waje cikin kasar da kuma samar da farashi mai rahusa ta yadda talaka zai iya siya,” inji shi.

Bagudu ya fada ma manoman shinkafa cewa kwanan nan gwamnatin jihar za ta fara samarwa tare da raba masu kananan injinan casar shinkafa, domin bunkasa ingancin shinkafar da suke kaiwa kasuwa.

“Tuni aka horar da matasa akan aiki da injinan wanda za su isar da wannan ilimi ga manoman shinkafa a kananan hukumomi 21 da ke jihar,” inji Bagudu.

Daya daga cikin manoman, Alhaji Abubakar Usman, ya fada ma gwamnan cewa sun samu girbi mai tarin yawa a wannan shekarar sannan cewa zai isa har zuwa badi.

KU KARANTA KUMA: Kakkausan lafazi: Minista Pantami ya yaba ma Hadiza Gabon kan neman gafarar Allah da ta yi

Usman ya kuma roki gwamnatin jihar da ta taimaka masu da taki, maganin kashe kwari da kuma injinan casar shinkafa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel