Kakkausan lafazi: Minista Pantami ya yaba ma Hadiza Gabon kan neman gafarar Allah da ta yi

Kakkausan lafazi: Minista Pantami ya yaba ma Hadiza Gabon kan neman gafarar Allah da ta yi

Ministan Sadarwa na Najeriya kuma shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami ya yaba ma fitacciyar jarumar Kannywood, Haliza Aliyu Gabon akan wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter.

A cikin rubutun, an gano jarumar na neman yafiyar Allah akan wani kakkausan martani da ta mayar wa da wani ma’abocin shafin Twitter bayan ya zarge tad a aikata zina.

Da fari dai jarumar ta mayar masa da zazzafan martani inda tace shakka babu da mahaifinsa ta yi zinar. Sai dai kuma bayan dan nazari da sharhi da mabiyanta suka yi, Hadiza ta fito ta bayar da hakuri inda ta nemi yafiyar Allah.

Hakan da jarumar ta yi ya burge mutane da dama ciki harda Sheikh Pantami, inda ya mayar mata da martani tare da fatan Allah ya cigaba da karewa da kuma yafewa.

Pantami ya jaddada cewa shakka babu Allah na son duk wanda ya yi kuskure kuma ya gane hakan sannan ya nemi yafiyarsa.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Hadiza Gabon ta nemi yafiyar Allah kan wani martani mai zafi da ta yi

Ga yadda ya wallafa a shafin nasa: "Wannan babban abun a yaba ne a nemi gafarar Allah bayan yin wani kuskure. Allah Madaukakin Sarki ya yafe mana ya kuma yi mana jagora tare da kare mu a gaba."

Tun da fari dai wani hoto da Hadiza ta dauka tare da Fati Washa da Rahama Sadau ne ya kawo magana. Sun dauki hoton ne a birnin Landan yayin da suka je karbar wata karramawa da aka yi musu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel