Kannywood: Hadiza Gabon ta nemi yafiyar Allah kan wani martani mai zafi da ta yi

Kannywood: Hadiza Gabon ta nemi yafiyar Allah kan wani martani mai zafi da ta yi

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Gabon, ta roki gafarar Allah kan wani subutar baki da ta ce ta yi da na sanin yin ta a shafin Twitter a ranar Lahadi.

Tun da farko dai Gabon ta mayar da martani ne ga wani mai amfani da shafin na Twitter ne, bayan ya yi mata kazafi a wani hoto da ta dauka tare da kawayenta kuma abokan sana’arta Rahama Sadau da Fati Washa wanda Rahaman ta wallafa a shafinta.

Hoton dai ya janyo kace-nace a shafukan sada zumunta musamman na Twitter da Instagram inda dukkan jaruman suka sanya a shafukansu.

Wani matashi ne ya fara cin zarafin jaruman inda ya zarge su da yin zina kafin su dauki hoton. Ba da jimawa ba ne ita kuma Hadizan ta mayar masa da martani da cewa da mahifinsa ma suka yi zinar.

Tuni dai Hadiza ta goge wannan sako ta kuma wallafa wani na neman gararar Allah SWT da yin da na sanin mayar da wancan martanin tun da fari.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Hukumar kwastam ta ce babu ranar bude iyakokin Najeriya

Fassarar sakon nata ya ce: "Astaghfirul Laah kan martanin da na mayar marar kyau kan wata amsar rashin da'a da wani ya ba ni. Na goge sakon kuma na nemi garafar Allah kan kokarin mayar da martani cikin fushi kan wani kuskuren da aka yi."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng