'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane da 'yan fashi 72 a Bauchi

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane da 'yan fashi 72 a Bauchi

Rundunar 'yan sanadan Najeriya reshen jihar Bauchi ta sanar da cewa ta kama wasu masu laifi 72 da ake zargi da tayar da hankulan jama'a a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Asabar.

Ana zargin masu laifin da aka kama da aikata miyagun laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami da sauransu. Rundunar atisayen 'Puff Adder' ce tayi nasarar kama masu laifin a cikin watan Oktoba.

A jawabin da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta bayyana cewa, "masu laifin sun amsa da bakinsu cewa sune keda alhakin fashin da ake yi a unguwannin garin Bauchi da suka hada da: Gida Dubu, Fadaman Mada, GRA, Waterboard Quarters, Turum, Madina, Bakaro da sauran wasu unguwannin cikin garin Bauchi.

"Kazalika sun amsa cewa sune suka kashe wani mutum mai suna Usman Mohammed a watan Afrilu, 2009, a Otal din Zaranda."

DUBA WANNAN: An karrama jaruma Fati Washa a Birtaniya

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar, wasu daga cikin jama'a sun tabbatar da cewa masu laifin ne suka taba yi musu fashi.

Ya kara da cewa daga cikin masu laifin da suka kama akwai mambobin wasu kungiyoyi biyu na 'yan ta'adda da suka kware wajen aikta manyan laifuka da suka hada da sata, sayen kayan sata, dabanci, mallakar muggan makamai da sauransu.

A cewarsa, an gurfanar da mutane 57 daga cikin jimillar masu laifin da aka kama, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike a kan sauran masu laifi 15.

Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kwace bindigu 10, carbin alburusai 5, adda 20, ababen motoci guda biyu da babura guda biyu da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel