Dalilin da yasa nake kwanciya da maza 15 kowacce rana a Abuja - 'Yar shekaru 15

Dalilin da yasa nake kwanciya da maza 15 kowacce rana a Abuja - 'Yar shekaru 15

Abin haushi, ban takaici da ban mamaki basa karewa a Najeriya. A wannan karon an samu wata yarinya mai shekaru 15 da ke kwanciya da maza 15 a kowacce rana domin kawai ta samu kudin da zata biya bashi.

Matashiyar wacce aka boye sunata na gaskiya saboda dalilan sirri ta bayyana cewa ta shafe watanni a cikin irin wannan yanayai a wani Otal da ke unguwar Lugbe a Abuja.

Matashiyar budurwar ta bayyana cewa ta tsinci kanta kane a cikin wannan mummunan hali bayan wata mata ta dauko ta daga kauyensu da ke jihar Anambra bisa alkawarin cewa za ta kawo ta Abuja domin ta saka ta a makaranta.

A cewar matashiyar, "Ina sanya guntun siket da karamar riga bisa umarnin Madam. Ina kwanciya da maza 15 a kan N1,000 kowacce rana, ina samun N15,000 a kowacce rana domin na biya Madam bashin kudin da ta ce ta kashe a kai na."

NAPTIP, hukumar yaki da safarar mutane ta kasa, ta ce a kalla kaso 75 na yaran da ake fataucinsu daga kauyuka zuwa manyan biranen Najeriya, suna fada wa hannun balagurbin mutane ne.

DUBA WANNAN: 2020: Buhari ya tsayar da ranar bude iyakokin Najeriya

Sashen Hausa na BBC ya wallafa cewa Otal din aka kai yarinyar a unguwar Lugbe, mazauni ne na talakawa da babu wata kyakyawar hanya ko kwalta da zata sada mutum da wurin.

BBC ta bayyana cewa wakilinta da ya ziyarci Otal din ya iske kananan yara da mata sanye da kayan da ke nuna surar jikinsu, yayin da samari da dama ke zaune a waje sun shaye-shaye.

Wakiliyar BBC ta yi basaja a zuwan ita ma tana da kananan yara mata da take son kawowa Otal din domin su yi aikin da irin matashiyar ke yi.

Wani mutum da ta iske a Otal din ya shaida mata cewa ta zabi daki guda a dakunan Otal din domin ajiye yaran idan ta zo da su tare da sanar da ita cewa zata ke biyan Otal din N10,000 kowanne sati.

Kazalika, ya yi mata kashedin cewa ta umarci yaran su ce shekarnsu na haihuwa sun kai 20 ko kuma sama da haka

BBC ta ce akwai Otal da dama da ake samun irin wadannan kananan yara da ake saka wa a cikin sana'ar karuwanci a unguwar Lugbe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel