Anambra: Akwai shaidanu a gidan gwamnati – Inji Willie Obiano

Anambra: Akwai shaidanu a gidan gwamnati – Inji Willie Obiano

Mai girma gwamnan jihar Anambra, Cif Willie Obiano, ya yarda cewa akwai wasu bakaken Aljanu a cikin gidan gwamnatin jihar. Gwamnan ya bayyana wannan ne a Yau, 2 ga Watan Nuwamba.

Gwamna Willie Obiano ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron addu’o’i da aka shiryawa jihar ta Anambra. Mabiya Anglikan ne su ka shirya wannan taro da aka yi wa lakabi da APRAS 2019.

Obiano ya yi wannan jawabi ne ta bakin sakataren gwamnatin jihar Anambra, Farfesa Solo Chukwubelu. An yi wannan taro ne a babban filin Dr. Alex Ekwueme da ke babban birnin Awka.

Gwamnan ya yi magana ne bayan abin da babban Faston Darikar na Angilika, Bishof Prosper Amah, ya fada. Malamin addinin ya tabbatar da cewa akwai Ifiritai a gidan gwamnatin Anambra.

KU KARANTA: Wani Gwamnan APC ya taya Buhari murnar nasara a kotun koli

Faston yake cewa wadannan aljanu su kan shigo gidan gwamnati wani lokaci su fita. Gwamnan ta bakin Solo Chukwubelu ya roki mutanen cocin su taya su da addu’a a kan wadannan aljanu.

Sakataren gwamnatin ya nemi Bayin Allah su dage da addu’a domin ganin aljanun sun fice daga gidan gwamnatin na din-din-din har abada domin a samu damar yi wa Talakawan Anambra aiki.

“A gidan gwamnati, akwai aljanun da ke shigowa su na tafiya. Mu na kiran ga coci su dage da addu’a saboda wadannan aljanu su kyale gidan gwamnati domin ayi aikin alheri.” Inji sa.

An rahoto shi ma Rabaren Alexander Ibezim ya na cewa: “Gwamnati su yaki aljanun da ke cikin gidan gwamnati, yayin da coci za su taimaka da yakar aljanun da ke waje masu kauda jama’a.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel