Nafisah Abdullahi ta fara makonta da hotuna cikin Khakin Sojoji

Nafisah Abdullahi ta fara makonta da hotuna cikin Khakin Sojoji

Fitacciyar ‘Yar wasar Hausan nan watau Nafisah Abdullahi, ta fara wannan makon da wallafa wasu hotunanta a shafin sada zumunta na Tuwita. Hotunan sun jawo surutun jama’a a shafin.

A Safiyar Litinin Nafisah Abdullahi ta daura hotunan na ta a shafinta na Tuwita. Sama da mutane 200 su ka nanata wadannan hotuna, yayin da mutane fiye da dubu uku su kace sun burgesu.

Daga karfe 11:00 na safen Ranar 28 ga Watan Oktoba zuwa yanzu wadannan hotuna sun karada wurare da dama a shafin sada zumunta, Nafisah dai tana da Mabiya fiye da dubu arba'in a shafin.

‘Yar wasan kwaikwayon ta rubuta: “Madalla, ka da a manta, yau ta ke Likitinin, kuma da ka da a manta a caba ado.” Tauraruwar ta dauki wannan hoton ne da wayar ta kirar IPhone 11 ‘yar yayi.

Nafisah Abdullahi ta fara makonta da hotuna cikin Khakin Sojoji
Nafisah Abdullahi cikin kayan Sojoji a gaban madubi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ke Duniya: Yaran Sakandare su na lalata a idanun Jama'a

Idan ba ku manta ba kafin nan fitacciyar Jarumar fim din ta yi Allah-wadai da wadanda su ka sa karya a gaba. Nafisah ta yi wannan magana ne bayan da wasu su ka rika surutu game da wayarta.

‘Yar wasan ta fito ta bayyanawa Duniya cewa ta na rike IPhone Xs da kuma IPhone 11 don haka tace ba ta bukatar ta saye wata sabuwar wayar IPhone domin kurum an fara yayin ta a Duniya.

Tauraruwar ta jawo hankali mutane su daina yawan damun kansu da wayar zamani. A shafin na ta na NafisatOfficial, an ga ta na taya Maryam Booth murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel