Asisat Oshoala ta zura kwallaye 2 a wasan Matan Barcelona da Madrid

Asisat Oshoala ta zura kwallaye 2 a wasan Matan Barcelona da Madrid

‘Yar wasar Najeriyar nan, Asisat Oshoala, ta jefa kwallaye biyu a wasan Barcelona da Real Madrid a Ranar Asabar 26 ga Watan Oktoba, 2019 a folon wasa na Municipal Nuevo Matapiñonera.

Fitaciyyar ‘yar wasan gaban ta taimakawa kungiyarta watau FC Barcelona femini wajen lallasa Real Madrid da ci hudu da nema. An buga wannan wasa ne a babban Birnin Sifen na Madrid.

‘Yar kwalon Najeriyar ce ta zama abin kallo a wasan ‘yan matan na Primera Iberdrola. Oshoala ta azabtar da ‘Yan matan Taawagar Víctor Fernández’ inda ta fara zura kwallo a minti na 43.

Ana dawowa hutun rabin lokaci kuma ‘yar wasan ta sake jefa wata kwallo a raga. A minti na 78 aka canji Budurwar da ta ke da kwallaye takwas a kakar bana a cikin wasanni goma sha daya.

KU KARANTA: Najeriya ta fara shirin kafa tarihi a Gasar cin kofin U-17

Hansen ce ta ba Jenni Hermoso kwallon da ta ci a wasan. Hernomoso wanda ta ci kwalla ta uku jiya ta na da kwallaye bakwai a karawar ta da Madrid. Daf da za a tashi wasa aka kara kwalla guda.

Aitana Bonmati ce ta ci wa Barcelona kwallon karshe a jiyan yayin da ake shirin hura tashi. Abin takaicin dai shi ne ‘Yaruwar Oshola watau Chidinma Okeke ta gamu da mummunan rauni a wasan.

Dole aka canza Chidinma Okeke da Laura Teruel. Idan aka yi rashin sa’a za a dauki dogon lokaci Okeke ba ta kara buga wasa ba. A bangaren maza, an dakatar da wasan El-Clasicco da aka sa a makon nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel