Shugaban 'yan kasuwan Ghana ya fadi matakin da za su dauka idan Najeriya ba ta bude boda ba

Shugaban 'yan kasuwan Ghana ya fadi matakin da za su dauka idan Najeriya ba ta bude boda ba

Clement Boateng shine shugaban kungiyar 'yan kasuwa na kasar Ghana. Ya yi jawabi a kan rufe iyakokin kasa da Najeriya ta yi da kuma yadda hakan ke shafar kasuwanci a kasarsa cikin wata zantawa da ya yi da Alexander Okere.

Boateng ya ce rufe iyakokin Najeriya ba shine abinda ya dace a yi ba domin hakan ya sabawa dokokin kungiyar kasashen Afirka Ta Yamma (ECOWA). Ya cigaba da cewa an kafa ECOWAS don inganta zirga-ziragan al'umma da kayayakin a tsakanin kasashen na Afirka Ta Yamma shi yasa kungiyarsu ta fitar da sanarwa na yin tir da rufe iyakokin da Najeriya ta yi.

DUBA WANNAN: Gidan Malam Owotutu: Gardawa 5 suka yi min fyade, na zubar da ciki har sau 3 - Budurwa

Da aka masa tambaya kan irin yadda rufe iyakokin ya shafe 'yan kasuwan Ghana, ya amsa da cewa "Ba wai Ghana kadai abin ya shafa ba; Ya shafa kusan dukkan kasashen ECOWAS da ke amfani da iyakokin ta Najeriya - Ya shafi Jamhuriyar Benin, Ivory Coast da Liberia. Kungiyar mu ta fitar da sanarwar ne don amfanin dukkan kasashen da abin ya shafa."

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan rashin daukan mataki da kwamiti na ECOWAS ba ta yi ba kan lamarin. Ya ce ya kamata Najeriya ta tattauna da kasashen da lamarin zai shafa kafin ta rufe iyakokin na ta.

Boateng ya ce 'yan kungiyarsa sunyi asarar dukiyoyi sosai duk da dai bai ambacci adadin ba.

Daga karshe ya ce idan har Najeriya ba ta bude iyakokinta ba dole za su dauki mataki, ya ce, "Za mu tafi wata kasar. Daya daga cikin dalilin da yasa muke kasuwanci da Najeriya shine kusancin mu da ita. Idan ka shigo a jirgin sama, za ka iso cikin mintuna 45 ka yi sayayan ka ka koma gida. Amma idan ba a bude bodar ba, zamu fara zuwa wasu kasahen kaman Dubai ko Turai. Za mu iya kauracewa Najeriya mu fara kasuwanci da Dubai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel