Matasan Arewa zasu yi zaman dirshan a kan tituna idan Buhari bai tabbatar da Magu ba

Matasan Arewa zasu yi zaman dirshan a kan tituna idan Buhari bai tabbatar da Magu ba

Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tabbatar da mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar mai cikakken iko.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugaban kungiyar, Gambo Ibrahim Gujungu ne ya bayyana haka yayin wani taron yan jaridu da suka kira a garin Kaduna, inda ya yi gargadin idan har Buhari bai tabbatar da Magu ba, toh fa zasu fita zanga zanga.

KU KARANTA: Jami’ar Kaduna ta fara binciken Malaman dake kwanciya da dalibai don cin jarabawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matasan sun yi kira ga fadar shugaban kasa, majalisar dokokin tarayya da duk sauran masu ruwa da tsaki dasu gaggauta tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC mai cikakken iko.

“Magu ya cancanci a tabbatar da shi wannan mukami duba da nasarorin daya samu a shekaru hudu da suka gabata, don haka muke kira ga shugaban kasa da yan majalisu dasu tabbatar da Magu domin kara samun nasar a yaki da rashawa.

“Babu shakka Magu ya kwato naira biliyan 939.51 daga hannun barayi tare da kadarori da darajarsu ta haura daruruwan biliyoyi, kuma ya yi sanadin daure masu laifi guda 1,636 wanda ba’a taba samun irin wannan a tarihin yaki da rashawa a Najeriya ba.

“Kuma muna da yakinin da mutane kamarsu Magu ne kadai yaki da rashawa a gwamnatin Buhari zata samu nasara saboda bashi da tsoro kuma mutumi ne mai gaskiya don haka muke kira a tabbatar da shi a mukaminsa.” Inji shi.

Daga karshe Gujungu yake basu yi mamakin yadda wasu ke yi ma Magu zagon kasa game da tabbatar dashi ba, musamman idan aka duba irin manyan mutanen daya daure, daga ciki har da tsofaffin gwamnoni 2.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel