San barka: Jarumi Adam A Zango ya ware kimanin miliyan 47 domin daukar nauyin karatun dalibai 101

San barka: Jarumi Adam A Zango ya ware kimanin miliyan 47 domin daukar nauyin karatun dalibai 101

Tsohon jarumin Kannywood, Adam A. Zango ya ware wasu miliyoyin naira domin daukar nauyin karatun wasu dalibai marasa gata.

A bisa ga wasu hotuna da rubutu da ya wallafa a shafinsa na Instagram, sun nuna cewa jarumin zai dauki nauyin karatun dalibai guda 101.

Daliban da suka amfana daga wannan shirin tallafi sun kasance yan babban makarantar sakandare, sannan kuma ya dauki nauyin karatun nasu ne har na tsawon shekara uku wato kenan daga SS1 zuwa SS3.

Gaba daya kudin karatun nasu da ya biya na wadannan shekaru ya kama naira miliyan N46, 714,520.

KU KARANTA KUMA: An gurfanar da wasu mutane 3 a gaban kotu kan zargin sace yaro dan shekara 4

Ga yadda ya wallafa a shafin nasa:

Jarumin ya jaddada cewa taimakawa mutane musamman kananan yara shine cikar burinsa da kuma taimakon marasa galihu.

Ya kuma bayyana cewa daga yanzu tawagarsa, ba za su boye duk wani aikin alkhairi da za su yi ba, yace za su yi aiki domin inganta rayuwar mata da yara marasa gata a fadin Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel