Dalilin da yasa jaruma Hafsat Idris ta fashe da kuka yayin wani taro

Dalilin da yasa jaruma Hafsat Idris ta fashe da kuka yayin wani taro

- Fitacciyar jarumar masana'antar Kannwood, Hafsat Idrsi wacce aka fi sani da barauniya ta fashe da kuka a wani taron karramata da aka yi

- Barauniya ta amsa kyautar Face of Kannywood da City Award ta shirya a birnin Legas

- Kukan da tayi a wajen ya jawo cece-kuce daga masoyanta tare ra'ayoyi mabanbanta

Fitacciyar jarumar Kannywood, Hafsat Idris, wacce aka fi sani da Barauniya ta fashe da kuka a wani taro. Barauniya, kamar yadda aka fi saninta dashi, ta fashe da kuka ne a yayin da tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya mika mata kyauta.

Shehu Sani ya mika kyautar Face of Kannywood ne da jarumar ta lashe a gasar City Movie Award na wannan shekarar da aka yi a birnin Legas.

KU KARANTA: Innalillahi: Masu fizgen waya sun hallaka matashi har lahira

Koda jarumar ta taso karbar kyautar, ta rufe fuskarta ne duk da ba a san dalilin hakan ba. Bayan karbar kyautar kuwa, sai aka mika mata abin Magana don ta mika sakon godiyarta. A take kuwa jarumar ta fashe da kuka a maimakon godiya bisa ga karramata da aka yi.

Wannan batu kuwa ya jawo hankulan mutane da dama. Mutane da yawa sun bawa kukan mabanbantan ra’ayoyinsu.

Hakazalika, abin ya zama batun tattaunawa a shafukan sada zumunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng