An kori wata daliba daga makaranta a kasar Saudiyya saboda yanayin halittar da Allah yayi mata
- An kori wata daliba daga makaranta a kasar Saudiyya saboda yanayin halittar da Allah yayi mata
- Dalibar dai tana fama da wata cuta da ta canja mata halitta, inda yanayin fuskarta yayi daban da irin na mutane
- Wannan abu da makarantar ta yi ya batawa mutane da yawan gaske rai, inda daga karshe ma'aikatar ilimi ta kasar ta bayar da umarnin sanyata a wata makarantar
An kori wata yarinya 'yar kasar Saudiyya daga makaranta saboda wata cuta da take fama da ita mai suna 'Treachers Collins Syndrome' wacce ta canja mata yanayin halittar kunne, ido da kuma wasu sassa na fuskar ta, hakan ya sanya halittar yarinyar yayi daban dana sauran mutane.
Yarinyar mai suna Loulwa bint Mohammed Al Fareeh, wacce take fama da wannan ciwon, an kore ta daga makarantar ne saboda wannan canjin halitta da cutar ta sanya mata.
Makarantar sunki amincewa su mayar da ita, inda suke korafin cewa bata da kunne da ido, mahaifiyarta ta bayyana musu cewa tana da su duka kawai dai sun rufe ne. Ta bayyana cewa abinda malamin yayi musu ya batawa yarinyar da mahaifinta rai.
Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa 'yar tasu ta kammala karatun da tayi a baya a kasar Birtaniya ba tare da samun matsala ko daya ba, amma a Saudiyya gashi yanzu tana samun matsala saboda halittar da ba ita ce ta baiwa kanta ba.
KU KARANTA: Shikenan fitsara ta kare: An daurawa mawakiya Nicki Minaj aure da masoyinta Kenneth Petty
Mahaifiyar ta kara da cewa 'yarta tana da matsala a ido da kunne amma kuma bata da matsala ko kadan a kwakwalwa, haka kuma tana fita da sakamako mai kyau a makarantar da ta kammala a birnin Landan.
Wannan lamari dai ya sanya mahaifiyar yarinyar kai karar makarantar zuwa ga ma'aikatar ilimi ta kasar ta Saudiyya da kuma hukumomin kare hakkin dan Adam na duniya.
Wannan labari na yarinyar ya bazu a ko ina a fadin kasar ta Saudiyya, inda ran mutane da yawa ya baci saboda wannan cin fuska da aka yiwa yarinyar.
A daya bangaren kuma shugaban ma'aikatar ilimi na kasar ta Saudiyya Dr. Hamad Al Sheikh ya bada umarni cikin gaggawa da a sanya wannan daliba a wata makaranta daban, hakan yasa hankalin mutane da yawa ya kwanta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng