Gaskiya matar Davido tayi sa’a da mahaifiyarsa ba ta raye, saboda uwar miji ke sa a saki mace – Jaruma mai sayar da maganin maza

Gaskiya matar Davido tayi sa’a da mahaifiyarsa ba ta raye, saboda uwar miji ke sa a saki mace – Jaruma mai sayar da maganin maza

Fitacciyar mai sayar da maganin karfin mazan nan, wato Hauwa Mohammed wadda aka fi sa ni da Jaruma ta ce, matar Davido, Chioma ta yi babbar sa’a kasancewar ba ta da suruka.

Jaruma ta ce: “ Uwar miji so da yawa ita ke sanadiyar mutuwar aure, har a kai ga yin saki.” Wannan maganar da Jaruma ta fadi ya janyo mata caccaka daga bakin mabiya shafukanta na sada zumunta.

KU KARANTA:Kwana daya da daukan hoto cikin makara, matashi ya mutu da gaske (Hotuna)

Saboda akasarin jama’ar da suka karanta sakon nata, sun fassara kalamanta ne a kan cewa tana murna saboda mutuwar mahaifiyar Davido.

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, wani matashi mai suna Isaac Terkende a jihar Benue ya rigamu gidan gaskiya kwana daya bayan ya dauki hoton wasa a cikin akwatin sanya gawa.

Isaac Terkende ya mutu cikin sa’o’i 24 da daukan wannan hoton. Majijoyi da dama sun bayyana mana cewa Isaac ya samu wani mummunan hadarin motane bayan kwana daya da daukar wannan hoto.

https://allure.vanguardngr.com/2019/10/mother-in-laws-are-the-cause-of-divorce-davidos-wife-chioma-is-lucky-not-to-have-one-jaruma-empire-says/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel