Ana zargin an yi son-kai wajen daukar aikin kuratan ‘Yan Sanda a Najeriya

Ana zargin an yi son-kai wajen daukar aikin kuratan ‘Yan Sanda a Najeriya

Bayan fitar da jerin mutane 10, 000 da ake sa rai za a dauka aikin ‘yan sanda a Najeriya, mun ji labari cewa wasu gwamnatocin jihohi sun yi tir da hanyar da aka bi wajen zakulo dakarun.

‘Yan Jaridu sun bi diddikin wannan jeri da aka fitar kwanakin baya a shafin Rundunar ‘yan sandan. Daga baya dai an cire sunayen har ta kai wannan ya jawo sabani tsakanin PSC da NPF.

A jerin da aka fitar na Dakaru 10000 a tsakiyar Watan Oktoba, an fahimci cewa an dauki mutum 528 aikin tsaron a jihar Nasarawa inda Sufetan ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya fito.

A jihar Katsina kuma, mutane 435 aka dauka aikin. Jihohin Borno da Bauchi sun kai kai kuka wajen hukumar PSC game da yadda Jihar Nasarawa mai kananan hukumomi 13 ta yi baba-kere.

A ka’ida ya kamata ace kowace karamar hukuma ta samu 12. Hakan na nufin Nasarawa za ta tashi da mutum 156, amma sai ga shi ta samu mutane fiye da 500 wanda da-dama ba su nemi aikin ba.

KU KARANTA: INEC sun ce sun hararo hadarin rigima tun kafin a fara zaben Kogi

Binciken da aka yi ya nuna cewa mutane 372 da aka ba wannan aiki a jihar Nasarawa ba su cike fam din neman aikin ‘dan sandan tun farko ba. Bisa dukkan alamu dai an bi ta bayan fage ne.

Borno ta samu mutum 274 ne a maimakon 324 da ya kamata a ba ta. Ita ma dai Bauchi an yi mata kauron mutum 8. Benuwai ta samu mutum 363, Kogi ta Kwara sun samu 304 da kuma 169 a jerin.

An ba jihar Neja mutum 396 a maimakon 300, sannan Filato ta tashi da 208. Jihar Adamawa kuwa sun iya samun 249 cikin 252. Jihar Gombe ta samu kari inda aka ba ta jami’ai 171 a madadin 132.

Irin su Kano wanda ya kamata a ba ta mutum 528, ta samu 403 ne. Kebbi da Kaduna sun samu karin mutane 20 zuwa 30. Jigawa, Taraba da Yobe sun samu sababbin Dakaru 193, 280, da 155.

Haka zalika an yi wa Sokoto da Zamfara kauro a jerin. A Kudu kuma Abia da Anambra sun samu 186 da 252. Yanzu dai an dakatar da batun daukar aikin a dalilin sabanin da ake ta faman samu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel