Oprah Winfrey ta ba Olufemi kyautar sabuwar wayar salula har gida

Oprah Winfrey ta ba Olufemi kyautar sabuwar wayar salula har gida

Mun samu labari cewa fitacciyar Attajirar nan, Miss Oprah Winfrey ta sayawa wani Matashin Najeriya Olufemi sabuwar wayar salula.

Mai kudin ta sanya wannan Bawan Allah farin ciki ne bayan da ta ba shi kyautar rangadediyar waya ‘yar yayi kirar IPhone mai tsada.

Idan ba ku manta ba kwanakin baya Miss Winfrey ta kai ziyara zuwa Kwalejin nan na Morehouse inda ta gana da wasu ‘Daliban makarantar.

Oprah Winfrey ta kai ziyara makarantar ne domin jaddada gudumuwar da ta saba badawa. A nan ne wasu su ka samu damar daukar hoto da ita.

Daga cikin wadanda su ka yi hoto tare da Oprah yayin da ta ke cikin motarta akwai Olufemi wanda ta yi ba’a a game da wayar da yake rikewa.

KU KARANTA: Buhari ya ware Biliyoyi a kasafin kudin 2020 domin a gyara wuta

Mista Olufemi ya bude baki yana cewa: “Ku na gani na tare da Oprah.” Inda ita kuma ta buda baki tace: “Eh ni ce nan a kwarababbiyar wayarka.”

Bayan wannan abu ya faru kenan sai ga shi wannan Mata da ke yi wa lakabi da Sarauniyar ‘yan jarida ta saye sabuwar waya ta aikawa Matashin.

Oprah ta rubuta: “Ya kai Olufemi, ba za mu bari ka rika ganin Duniya a cikin kwarababbiyar waya ba. Na san tabbas kyamarar wayar za ta burge ka.”

Oprah Winfrey ta na cikin Matan da su ka fi kowa kudi a Duniya. Hasashe ya nuna cewa a yanzu, Ba-Amurkiyar ta ba sama da Dala biliyan 2.7 baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel