Akwai laifin Iyaye wajen fasikanci da Yaran Makarantun Jami'a - Garba

Akwai laifin Iyaye wajen fasikanci da Yaran Makarantun Jami'a - Garba

Farfesa Ibrahim Garba, wanda shi ne shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya yi wata hira da gidan Rediyon Najeriya na Kaduna, FRCN, inda ya yi magana kan barnar da ake yi a jami’a.

Ibrahim Garba ya zargi yadda wasu Iyaye ke dankawa ‘Ya ‘yansu makudan kudi da motocin hawa da wayoyin zamani a matsayin daya daga cikin dalilan da su ka sa ake lalata da ‘Ya ‘yan na su.

Farfesa Garba yake cewa ba wadannan yara abin Duniya ya sa ba su iya zagewa su yi karatun da ya dace domin su ci jarrabawa, a dalilin haka sai su buge da bin malamai domin su samu nasara.

“Jami’a ba kamar Sakandare ba ce, domin ‘daliban jami’a a sake su ke da tunanin cewa sun girma. Domin babu da damar takurawa ‘dalibai, sai mu ka kirkiro hanyoyin da za a kare su.” Inji Garba.

KU KARANTA: Dalilin da zan ba Mata rabin kujerun mukamai a mulki na – Gwamna

Garba ya zargi rashin tarbiya a wannan zamani daga cikin wasu dalilan tabarbarewar ‘yan mata. “Duk wannan ya jawo yaran su ka sa lalaci har su ke neman kowace irin hanyar cin jarrabawa.”

Shugaban jami’ar ya kara da cewa: "A dalilin haka sai su mika kansu gaban gurbatattun Malamai domin su ci jarrabawa. Amma duk da haka mun dauki tsauraran matakin hukunta masu laifi.”

Farfesan ya na cewa jami’ar Ahmadu Bello ba ta dauki wannan mummunan aiki da wasa ba inda ta yi tanadin hukunci mai tsauri ga duk wanda aka kama yana aikata wannan danyen aiki.

A cikin hanyoyin da aka bi shi ne maida hankali kan walwalar Dalibai. A cewarsa, wannan karo jami’ar ta gina dakuna rututu domin kwanan Dalibai. Sannan an yi maganin kungiyoyin asiri.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel