Yanzu- yanzu: Zaki ya kwace daga ma'adanarsa a gidan zoo din Kano

Yanzu- yanzu: Zaki ya kwace daga ma'adanarsa a gidan zoo din Kano

- Tashin hankali da tsoro sun shiga zukatan jama'ar yankin titin Zoo da ke Kano

- Da yammacin yau Asabar ne Zaki ya kubcewa masu kula dashi inda ya tsere

- Rundunar 'yan Sanda sun bazama neman Zakin tarre da kwantarwa da mutanen yankin hankula

Tashin hankali da tsoro sun samu mutanen tsakiyar birnin Kano a daren yau Asabar, 19 ga watan Oktoba 2019.

Zaki ya kwace daga hannun masu kula dashi daga gidan Zoo din Kano a daren yau Asabar.

KU KARANTA: Pantami ya samu lambar yabo

Majiya ta sanar da jaridar Daily Nigerian cewa, Zakin ya kubce ne bayan da aka dawo dashi wani shirin noma da kiwo a yammacin nan. Masu kula dashi sun yi kokarin maidashi amma ya rinjayesu tare da fin karfinsu.

Duk da cewa, hukumar gidan zoo din bata ce komai akan aukuwar hakan ba, amma mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Amma ya ce, har yanzu Zakin yana nan cikin gidan Zoo din duk da ba a san inda yake ba.

Ya kara da cewa, an tura runduna don nemo Zakin tare da 'yan sandan da zasu kwantar da hankulan jama'ar yankin.

Kiyawa ya ce, ba a samu rahoton raunata kowa da Zakin yayi ba har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel