Babu yunwa a Najeriya, N30 ta isa mutum ya ci abinci ya koshi - Ministan Noma
A cikin makon nan ne sabon ministan noma da raya karkara, Alhaji Sabo Nanono, ya bayyana cewa babu yunwa a Najeriya tare da bayyana cewa jama'a ne kawai ke jawo wa kansu da kansu masifa.
A yayin da jama'a ke tsaka da sukar da ministan a kan fadin hakan, sai ga shi ya kara bayyana cewa akwi wuraren da mutum zai ci abinci ya koshi a Naira talatin, N30, a cikin Kano.
Wadannan kalamai na Nanonon basu yi wa jama'a, musamman mazauna Kano, dadi ba, lamarin da yasa suka shiga sukarsa tare da bayyana cewar bai san halin da jama'a ke ciki ba shi yasa yake fadin wadannan maganganu.
Ganin korafin da sukar da Ministan ke sha a wurin jama'a ne yasa gidan radiyon Freedom da ke Kano ya kira shi domin jin ta bakinsa, inda shi kuma ya kara tabbatar musu cewa ya fadi hakan kuma yana nan a kan bakansa, ba zai janye abinda ya fada ba.
DUBA WANNAN: Jakadan Najeriya ya bukaci a tsige gwamnan PDP a arewa, ya bayyana dalili
"Kamar yadda na fada, akwai wurin da zaka ci abinci ka koshi a N30 a Kano, idan mutum ya zo Kano zan nuna masa.
"Babu yunwa a Najeriya, idan kana maganar yunwa, akwai wuraren da mutum sai ya kwana 10 bai ci abinci ba. Amma a Najeriya babu yunwa, ni abinda bana so shine jama'a suke jawowa kansu masifa da bala'i haka kurum," a cewar Nanono, a hirarsa da gidan radiyon Freedom da ke Kano.
Ministan ya kara da cewa idan aka dauke wasu sassan arewa maso gabas da ke fama da matsalar Boko Haram, babu wani bangare a Najeriya da ake fama da yunwa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng