Shah Rukh Khan da sauran jaruman fim da kasar Saudiya ta karrama

Shah Rukh Khan da sauran jaruman fim da kasar Saudiya ta karrama

Fitaccen jaruman finan finan Indiya na masana'antar Bollywood, Shah Rukh Khan, na daya daga cikin manyan jaruman fina-finan kasashen duniya 15 da kasar Saudiyya ta karrama da wata lambar yabo ta Joy Excellence Awards a wani biki da aka gudanar a ranar Litinin.

Jarumin wanda ya shahara musamman a fina-finan soyayya a masana'antar Bollywood, ya wallafa sakon godiya ga kasar Saudiyya a zauren sada zumunta na Twitter, tare da watsa hotunan yadda bikin ya gudana.

A yayin gabatar da jawabansa kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, jarumi Shah Rukh ya bude da 'Bismillah Al-rahman Al-rahim,' wato 'Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai'. Bayan haka ya yi gaisuwa irin ta addinin musulunci a taron da aka gudanar a babban birni na Riyadh.

Babu shakka jarumi Shah Rukh Khan ya kasance musulmi ne, kuma hakan bai sanya ya na nuna bambanci ga sauran addinai don ko matarsa Gauri Khan mabiyar addinin Hindu ce kuma sun shafe shekara 28 suna tare.

KARANTA KUMA: Haihuwar 'ya'ya barkatai rashin fahimtar addini ne - Issoufou

Sauran jaruman duniya da aka karrama a taron na Joy Excellence Awards sun hadar da; wata fitacciyar jarumar kasar Masar, Ragaa El Gedawy, da jarumin fim din Game of Thrones da Aquaman, Jason Momoa, Jean-Claude Van Damme, Jackie Chan da sauransu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng