Tallafin da ake bayarwa bai isowa garemu, manoman shinkafa a Kano sun koka da gwamnatin tarayya

Tallafin da ake bayarwa bai isowa garemu, manoman shinkafa a Kano sun koka da gwamnatin tarayya

Wasu manoman shinkafa a jihar Kano sun bayyana korafinsu game da tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa ga manoma, inda ta ce bai isowa zuwa gareta. Tallafin da manoman ke magana a kai shi ne wanda bankin CBN ke bayarwa.

Daya daga cikin manoman shinkafan, Dr Aminu Baba Nabegu wanda ya fadawa kungiyar masu kishin Kano ta KCCI a lokacin da suka ziyarci gonarsa dake kauyen Garun Babba, ya ce: “Hakikanin manoman shinkafan ba su samaun wanna tallafin na gwamnatin tarayya yana kai wa garesu.”

KU KARANTA:APC jam'iyya ce ta gagaruman makaryata - Gwamnan PDP

Nabegu ya ce duk da yana noma eka kusan 200,000 amma bai taba samun tallafi daga gwamnatin tarayya ba ko na sisin kwabo. Inda yake cewa akasarin masu amfana da tallafin ba manoma bane.

Dr Baba ya ce: “A ko wace shekara ina kashe sama da naira miliyan 700 domin yin noma a gonata. A ko wane eka daya ina samun akalla buhu 250 lokacin girbi. Sama da mutane 5000 ke ci daga aikin da suke a gonata, amma ban taba samun tallafi daga wurin gwamnati ba.”

Ya yi kira ga gwamnatin da ta duba tsarin yadda ake bayar da tallafin domin yin gyara a kansa. Wani manomin mai suna Alhaji Zakari Saidu Garun Babba, shi ma ya yi korafi a kan wanna tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa.

A cewarsa, kudin da gwamnatin tarayya ke warewa sashen noma a kasafin kudin shekara yayi kadan, don haka babu yadda za ayi bangaren noma ya wadata da abubuwan da yake bukata a cikin shekara guda.

https://www.dailytrust.com.ng/kano-rice-farmers-to-fg-your-interventions-not-reaching-us.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel