Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addini a wata jihar arewa, sun bukaci iyalansa su fara tara kudin fansa

Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addini a wata jihar arewa, sun bukaci iyalansa su fara tara kudin fansa

Yan bindiga a ranar Talata, 15 ga wata Oktoba, sun kai mamaya garin Malum, wani yanki na karamar hukumar Ardo-Kola da ke jihar Taraba sannan suka yi garkuwa da Reverend Solomon Jediel.

Yan bindigan bayan sun yi gaba da mai wa’azin sun kira iyalinsa sannan suka sanar dasu cewa su fara tara kudi domin biyan fansar sa.

Matar malamin, Lucy Solomon, wacce tayi bayanin lamarin nab akin ciki ga Channels Televison cikin harshen Hausa tayi bayanin cewa masu garkuwan na ta harbi ba kakkautawa a sama, inda suka farfasa wundunan gidansu sannan suka yiwa ahlin gidan mugun duka.

“Muna shirin bacci ne lokacin da mijina ya bukaci na leka taga sannan sai na hangi masu garkuwan. Da suka kusa sosai, sai suka haska mana toci sannan suka bukaci mijina da ya fito ya bisu ko kuma su harbe shi.

“Sai ya basu hadin kai sannan ya bude kofar. Sai suka fara dukkan duk wani ahlin gidan. Sun yi arazanar kasha ni sannan suka nemi na kudaden da ke gida, na kawo sannan suka tafi da kudin, da mijina da kuma takardun makarantar ‘yata.

“Daga bisani sun kira dana, inda suka umurce shi da ya faa tara kudi doomin sakin mahaifinsa,” tayi bayani.

KU KARANTA KUMA: Bukatun Ma’aikatan Najeriya ya fi karfin Gwamnatin Tarayya - Inji Chris Ngige

Reverend Philip Jedian, Shugaban cocin yankin, da yake martani ga lamarin, yace abun yayi yawa. Sannan yayi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su tashi su isar da hakkinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sace Reverend Solomon na zuwa ne kwanaki biyar bayan gwamnan jihar, Darius Ishaku ya bayyana cewa an sace akalla mutane 100 cikin watanni tara a jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel