Ali ya ga Ali: Saraki ya hadu da Osinbajo da Tinubu a Lagas

Ali ya ga Ali: Saraki ya hadu da Osinbajo da Tinubu a Lagas

Hotunan Sanata Bukola Saraki a lokacin da suke musabaha tare da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da babban jigo jam'iyyar All Progressives Congess (APC) Asiwaju Bola Tinubu ya yi fice a shafukan sadarwa.

A cikin hotunan an gano tsoho shugaban majalisar dattawan na ta murmushi tare da mataimakin shugaban kasar da kuma tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Taron ya kasance bikin zagayowar ranar haihuwar wata shaharariyar yar kasuwa, Hajia Bla Shagaya karo na 60 a jihar Lagas.

Ali ya ga Ali: Saraki ya hadu da Osinbajo da Tinubu a Lagas
Saraki ya hadu da Osinbajo da Tinubu a Lagas
Asali: Facebook

Shigowar Saraki ya sa dakin taron ya dauki sowa inda mutane ke ta gaishe shi suna iun 'Oloye', saautar da yake ci.

Ya halarci taron ne tare da uwargidarsa, wacce ta kuma kasance ma'assashiyar gidauniyar Wellbeing, Hajia Toyin Saraki.

Duk da cewar ya tafi hutu daga harkar siyasa, har yanzu ana jin dunan Saraki a mafi akasarin lamuran da suka shafi siyasar kasar da kuma kafofin watsa labarai.

KU KARANTA KUMA: Rajista biyu: ‘Yar takara ta na neman kotu ta hana Bello da APC tsayawa zabe

Har yanzu tsohon gwamnan na jihar Kwara na cikin lamura tsundum domin a kwanan nan ne jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta nada shi mukami domin ya hada kan magoya bayan jam'iyyar a Bayelsa da jihar Kogi yayinda ake shirin zaben gwamna a jihohin guda biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel