Dattawan Kano sun bayyana damuwa kan yaran da aka ceto daga hannun masu safarar mutane a jihar Anambra

Dattawan Kano sun bayyana damuwa kan yaran da aka ceto daga hannun masu safarar mutane a jihar Anambra

Wata kungiyar dattawan jihar Kano, KCCI, ta yi Allah wadai dangane da sace wasu kananan yara 9 na jihar tare da mayar da su addinin kirista da wata muguwar kungiyar masu garkuwa da mutane 'yan kabilar Ibo ta yi.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu Inyamurai 6 da suka amsa laifin sace kananan yaran kuma suka sayar da su a birnin Onitsha na jihar Anambra da ke Kudancin Najeriya.

Cikin wata sanarwa da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Usman Tofa, ya ce sace kananan yaran wata babbar musiba ce duba da girman laifin mai munin gaske na sauya akida da miyagun suka aikata.

Ba ya ga bayyana munin ta'addancin garkuwa da mutane, kungiyar ta yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su mike tsaye wajen daukar mataki kan wannan mummunan lamari da ya ci karo da yarjejeniyar zaman lafiya ta bai wa kowa damar yin addini bisa ga ra'ayi.

Sauran mambobin kungiyar da suka sanya damuwar al'ummar jihar Kano sun hadar da; Engr. Bashir M. Borodo, Dr. Tijjani Naniya, Alhaji Shehu Muhammad, Hajiya Binta Sarki Mukhtar, Alhaji Muhammad S. Nanono, Alhaji Abdurrahman Umar da kuma Alhaji Sabi’u Ibrahim.

KARANTA KUMA: Kasar Nijar ta haramta shigowar zuwa shinkafa Najeriya

A rahoton da jaridar BBC Hausa ta wallafa, rundunar 'yan sandan Kano ta ce ta ceto kananan yara ne 'yan asalin jihar Kano wadanda aka yi garkuwa da su a jihar Anambra bayan an sace su daga Kano.

Kwamishinan ‘yan sandan na Kano Ahmed Ilyasu ya ce kananan yaran da shekarunsu ya kama daga 2 zuwa 10, an sace su ne a lukota daban-daban a jihar, inda wasu ma aka sace su tun a shekarar 2014, amma a yanzu aka gano su a jihar Anambra, inda aka ci kasuwarsu su.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel