Sunan wadda ta la'ka wa Najeriya suna da sauran abubuwa 9 da ya kamata ku sani a kan kasar

Sunan wadda ta la'ka wa Najeriya suna da sauran abubuwa 9 da ya kamata ku sani a kan kasar

A yau jaridar Legit.ng ta kawo muku wani takaitaccen tarihin kasar Najeriya. Idan a ba a manta ba, a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar da muke ne a gudanar da bikin murnar cikar kasar shekaru 59 da samun 'yancin kai.

Ga wasu ababe na tarihi da ya kamata duk wani dan kasa mai kishi ya sani a kan Najeriya kamar haka:

  1. Najeriya ta kasance kasa ta 32 cikin jerin sahun kasashen duniya mafi girma a duniya idan an kalli mahangar fadin kasa.
  2. Marigayi Benedict Odiase, wani tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda, shi ne ya hada kidan da aka rare wa Najeriya taken girmama kasa da a turance a ke kira National Anthem.
  3. Wasu 'yan Najeriya hudu ne suka shirya kalaman da ake amfani da su wajen rera taken girmama kasar nan da suka hadar da; Dr. Omoigui, John Ilechukwu, Eme Etim Akpan, B.A Ogunnaike, da kuma P.O Aderibigbe
  4. Akwai jami'o'i mallakin gwamnatin tarayya guda 37, haka kuma akwai jami'o'i daidai wannan adadi mallakin gwamnatin jihohi, inda kuma akwai fiye da jami'o'i 50 a kasar masu zaman kansu.
  5. A kidayar da aka yi a shekarar 2006, an kayyade adadin al'ummar Najeriya a kan miliyan 140,431,790. Sai dai a yanzu ana kiyasin cewa adadin al'ummar kasar ya doshi kusan miliyan 200.
  6. Flora Shaw, ita ce laka wa Najeriya sunanta na 'Nigeria', matar Lord Lugard, daya daga cikin turawan kasar Birtaniya da suka yi wa kasar nan mulkin mallaka.
  7. Najeriya ita ce kasar da ta fi kowace kasa yawan adadin al'umma a nahiyyar Afirka, kuma ita ce kasar da ta ke kan sahu na bakwai a jerin kasashen duniya masu tarin al'umma kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Ganduje ya zabi kwamishinoni na jihar Kano

8. A ranar 1 ga watan Janairun 1901 ne kasar Najeriya ta kasance a karkashin turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya.

9. An shafe shekaru uku ana yakin ballewar yankin Biyafara, inda Kanal Odumegwu Ojukwu ya nemi ballewar yankin daga Najeriya a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 1967 domin kafa kasar Biafra.

10. Najeriya ta shafe tsawon shekaru 33 tana kan tsari na mulkin soja daga shekarar 1966 zuwa 1999, inda da ta koma tsarin dimokuradiyya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel