Haraji: Jihohin Najeriya 36 da Abuja sun tara N691.11bn a watanni 6 na shekarar 2019 - NBS
Tattalin arzikin Najeriya ya karu a watanni shidan farko na bana, a cewar wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS ta wallafa a kan adadin kudaden shida da jihohi 36 na kasar da kuma garin Abuja suka tara.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, NBS cikin wallafar ranar Juma'a da ta gabata a kan shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa, jihohin kasar 36 da kuma garin Abuja sun tara kimanin naira biliyan 691.11 a rubu'in farko da na biyu na shekarar 2019 da muke ciki.
Hukumar ta ce naira biliyan 94.2 ne a ka samu ya karu a kudin shiga wanda ya yi daidai da kaso 15.78 cikin dari a bana idan an kwatanta da na bara da kasar ta tara naira biliyan 596.91 a rubu'i na uku da na hudun shekarar 2018.
Alkalumman Hukumar NBS sun tabbatar da cewa, jihohi 31 da kuma Abuja sun samu kari a kudaden shiga da suka tara yayin da na jihohi biyar ya ragu cikin tsawon lokacin da ta yi bitar yawan kudin haraji da aka tara a kasar.
KARANTA KUMA: Lafiyar ido da amfanin tafarnuwa 7 ga lafiyar dan Adam
Har wa yau NBS ta ce bashin waje da ya yi wa Najeriya katutu yana nan a kan Dala Biliyan 4.23 yayin da bashin cikin gida ya tuke kan Naira Tiriliyan 3.85 a karshen shekarar 2018.
Dalla Dalla ga yadda jihohin kasar suka tara haraji kamar yadda Hukumar Kididdiga ta kasar ta fitar a shafinta na yanar gizo:
- Legas - N263.25bn;
- Ribas - N151.8bn;
- Delta - N145bn;
- Akwa Ibom - N106.7bn;
- Abuja - N72.8bn;
- Bayelsa - N71.6bn;
- Kano - N58.5bn;
- Kaduna - N54.7bn;
- Ogun - N48bn;
- Edo - N47.3bn;
- Ondo - N47.2bn;
- Oyo - N42.1bn;
- Sakkwato - N38.8bn;
- Benuwe - N38.1bn;
- Imo - N37.4bn;
- Kwara - N36.6bn;
- Neja - N36.1bn;
- Enugu - N35.7bn;
- Katsina - N35.4bn;
- Cross Rivers - N33.9bn;
- Jigawa - N33.9bn;
- Bauchi - N33.7bn;
- Borno - N33.6bn;
- Abia - N33.5bn;
- Anambra - N32.2bn;
- Kogi - N31.6bn;
- Filato - N30.7bn;
- Kebbi - N30.3bn;
- Adamawa - N28.2bn;
- Yobe - N27.2bn;
- Zamfara - N27.1bn;
- Nassarawa - N26.6bn;
- Ebonyi - N26.5bn;
- Taraba - N25.7bn;
- Ekiti - N25bn;
- Gombe - N25bn;
- Osun - N20.2bn.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng