Sojoji sun kubutar da dalibai 6 da aka sace a jihar Kaduna, Hoto

Sojoji sun kubutar da dalibai 6 da aka sace a jihar Kaduna, Hoto

Dakarun soji na rundunar atisayen 'Thunder Strike' sun kubutar da daliban makarantar sakandire ta jeka ka dawo da ke garin Gwagwada a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna, da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa makaranta da safiyar ranar Alhamis.

Kamafanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa mataimakin darektan hulda da jama'a na rundunar soji ta daya da ke Kaduna, Kanal Ezindu Idimah, ya tabbatar da kubutar da daliban ga manema labarai a Kaduna ranar Alhamis.

Idimah ya bayyana cewa dakarun soji sun kubutar da wasu yaran mota su uku tare da kashe hudu daga cikin masu garkuwa da mutanen.

"Dakarun soji da ke sintiri a yankin sun samu labarin cewa wasu 'yan bindiga da suka addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna sun yi awon gaba da wasu dalibai yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makaranta.

"Nan da nan sojojin suka bi sahun 'yan bindigar da suka sace daliban kuma suka yi nasarar cimma su tun kafin su yi nisa.

"Masu garkuwa da daliban sun bude wuta a kan tawagar rundunar sojoji da suka hango ta nufo su, kuma nan take dakarun sojin suka mayar da martani

"Biyo bayan musayar wutar da aka yi, an kashe daya daga ciin 'yan bindigar yayin da sauran abokansa suka gudu cikin daji da raunukan harbin bindiga" a cewar Idimah.

Ya ce an kubutar da dukkan daliban da aka sace ba tare da wani abu ya same su ba tare da bayyana cewa tuni aka damka su ga iyayensu.

Kazalika, a wani harin da dakarun soji suka kai wasu gungun 'yan bndiga a Soho Gaya da ke karamar hukumar Chikun, lamarin da ya sanadiyar wasu daga cikin 'yan ta'addar.

Sojoji sun kubutar da dalibai 6 da aka sace a jihar Kaduna, Hoto
Sojoji sun kubutar da dalibai 6 da aka sace a jihar Kaduna, Hoto
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel