Kotu a jihar Kano ta damke wani Malamin jami'a da ta kama shi yana kokarin lalata da dalibar shi

Kotu a jihar Kano ta damke wani Malamin jami'a da ta kama shi yana kokarin lalata da dalibar shi

Wata kotun majistare da ke zama a Kano a ranar Talata, tayi umurnin tsare wani lakcara mai shekara 36, Ali Shehu, a gidan yari kan cin amana da kuma kokarin lalata da dalibarsa mace.

Wanda ake zargin, wanda ya kasance lakcara a makarantar kimiyya na jihar Kano, na fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume guda biyu na cin amanar aiki da kuma kokarin aikita wani laifi, wanda yayii karo da sashi na 95 da 98 na kundin doka.

Jaridar Vanguad ta ruwaito cewa alkalin kotun, Muhammad Idris yayi umurnin tsare wanda ake zargin sannan ya daga zaman har zuwa ranar 15 ga watan Oktoba domin yanke hukunci.

Da farko dan sanda mai kara, ASP Badamasi Gawuna, ya fada ma kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Agusta a Kano.

Yace hakan ya biyo bayan wani aiki da hukuma sauraron korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta gudanar.

KU KARANTA KUMA: An bawa malaman Islamiyya 6 masauki a gidan gyaran hali a Kaduna

Gawuna yace a wannan rana da misalin 11:00 na safe, wanda ake zargin wanda ya kasance lakcara a makarantar kimiyya na Kano, ya dauki wata dalibarsa mace zuwa Ummi Plaza a Kano, domin ta taimaka mashi wajen makin jarrabawar zangon karshe.

“A cikin haka, wanda ake zargin ya amince da taba wa dalibar tasa matancinta,” inji dan sandan.

Wanda ake zargin ya amince da aikata laifin da aketuhumarsa a kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: