Za mu yi nazarin shari’ar Bauchi don mu dauki mataki - Lauyan APC

Za mu yi nazarin shari’ar Bauchi don mu dauki mataki - Lauyan APC

Babban Lauyan da ke kare tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da jam’iyyar APC a kotun da ya yi sauraron karar zaben jihar Bauchi ya yi jawabi bayan an yanke hukunci jiya.

Babban Lauya Ishiaku Dikko ya bayyana cewa za su duba hukuncin da kotu ta yanke, sannan su san matakin da za su dauka a gaba. Ishiaku Dikko ya bayyana mana wannan ne a jiya Litinin.

A Ranar 7 ga Watan Oktoban 2019 ne Alkali ya yi watsi da karar da APC da ‘dan takararta su ka shigar a game da zaben gwamnan jihar Bauchi inda jam’iyyar adawa PDP ta karbe mulki a bana.

Dikko SAN wanda ya shigar da kara a madadin APC da tsohon gwamnan ya fadawa Manema labarai cewa akwai bukatar su duba hukuncin da aka yi, su kuma tattauna kafin a dauki mataki.

Shi kuma a na sa bangaren, babban Lauyan gwamna mai-ci na PDP Chris Uche, ya ji dadin hukuncin da kotu ta yi inda ya ce su na sa rai kotu za ta sake fatali da karar idan aka daukaka ta.

KU KARANTA: An ba Kauran Bauchi gaskiya a kotun karar zaben 2019

“Yau kuri’un da mutanen kirkin jihar Bauchi su ka ba gwamna Bala Mohammed ya samu tabbaci daga kotu. Mun ji dadin adalcin da kotun sauraron korafin zabe ta yi mana” Inji Lauya Uche SAN.

Lauyan ya ce: “Wannan kara ce da ba ta da hujjoji masu yawa da karfi. Idan su na ganin abin da ya dace shi ne a daukaka kara, sai su tafi kotun na gaba, amma abin takaicin shi ne haka za su kare."

Mai kare gwamna Bala Mohammed din ya yi wa APC albishir cewa a kotun daukaka kara ma ba za su kai ga ci ba domin Alkalan kotun ba za su sake karbar wasu sababbin hujjoji a karar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel