Kotun Majistare ta tsare Malamai a gidan kaso a Jihar Kaduna
Wani karamin kotun Majistare da ke aiki a Kaduna ta tsare Malamai shida na makarantar musuluncin nan na Ahmad Bn Hambal Islamiyya da ke cikin Garin da ‘yan sanda su ka kama.
Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a jiya, 7 ga Watan Oktoba 2019, an gurfanar da Malaman addinin a kotun Majalistare na 16 da ke Kaduna a gaban Alkali Musa Lawal Mohammed.
An shigo da wadannan Malamai harabar kotu ne da karfe 1:00 inda aka soma zama da karfe 2:00 na rana. Alkali mai shari’a Musa Lawal Mohammed ya kuma tashi ne da bayan sa’a guda da rabi.
Wadanda aka gurfanar a gaban kuliya sun hada da; Ismail Abubakar, Umar Abubakar, Abdul’azeez Adam, Abubakar Muktar. Ragowar su ne; Abdullahi Auwal da kuma wani Salisu Ibrahim.
Lauyan hukumar ‘yan sanda, Hassan M Malan, ya fadawa kotu cewa ana zargin wadannan mutanen ne da kitsa laifi, tsare mutane, da kutun-kutun da kuma mugunta da yin ba daidai ba.
KU KARANTA: An yi Allah-wadai da amfani da ‘Daliban da ake yi a Makarantu
Hassan .M. Malan ya kuma sanar da Alkalin kotun cewa yanzu haka ‘yan sanda su na cigaba da binciken laifukan wadanda ake zargin. A na sa bangaren, Lauyan wanda ake tuhuma, ya kare su.
Sani Shehu Surajo wanda shi ne ya tsayawa wadanda ake zargin ya fadawa kotu cewa babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna wadanda ake tuhumar sun aikata laifukan da ake jefe su da su.
Lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Shehu Surajo ya yi kokarin rokon kotu ta bada dama a saki wadannan Bayin Allah daga cikin gidan yari, a cigaba da bincikensu a ofishin ‘yan sanda.
Mai kare hukuma ya maida martani cewa ragar hukumar ta cika don haka a cigaba da tsare su a kurkuku. Dayan Lauyan yace zai nemo beli a babban kotu bayan dage karar zuwa 29 ga Wata.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng