A gaggauta daukar mataki kan keta haddin dalibai da malamai ke yi a jami'o'i - Aisha Buhari

A gaggauta daukar mataki kan keta haddin dalibai da malamai ke yi a jami'o'i - Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari, ta yi kira ga muhukunta da kuma masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar mataki a kan yadda malamai ke keta haddin dalibai mata a jami'o'i da makarantun gaba da sakandire na kasar.

Hajiya Aisha ta yi kiran ne a daren ranar Litinin da ta gabata yayin halartar wani shiri da kafar watsa labarai ta BBC Hausa ta yi dangane da yadda malaman makarantun gaba da Sakandire a Najeriya ke lalata da dalibai 'yan mata domin ba su maki a jarrabawa.

Shirin kafar watsa labaran mai lakabin BBC Africa Eye, ya shafe tsawon shekara guda yana gudanar da bincike domin bankado yadda malaman jami'a ke lalata da dalibai 'yan mata da ya zuwa yanzu ya kai matuka wajen jan hankulan jama'a a shafukan sada zumunta.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, uwargidan shugaban kasar ta yi babatu gami da bayyana damuwa a birnin Ikon Legas, a kan yadda malaman makarantun gaba da sakandire musamman na jami'o'i ke yin lalata da dalibai mata, da ya zamto wata al'ada mai munin gaske a dukkanin sassan kasar.

KARANTA KUMA: Sunayen zababbun kwamishinoni 17 sun isa gaban majalisar dokokin jihar Neja

Hajiya Aisha wadda wata lauya takwararta ta wakilta a yayin shirin, Aisha Rimi, ta yi Allah wadai da yadda keta haddin dalibai mata a jami'o'i ya zamto wata mummunar annoba ta ruwan dare da ta haddasa koma baya ga tsarin karatu da neman ilimi a kasar.

Ta jaddada cewa a kwai dokoki da kundin tsariin mulkin kasa ya yi tanadi domin bai wa mata kariya da tsare 'yancin su gami da martaba daga dukkanin wani cin zarafi ko kuma keta haddi, lamarin da ta ce dokokin ba za su yi tasiri ba face wadanda abin ya shafa sun fito karara domin a kwatar masu 'yanci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel